Banbanci Fassarar Indian Hausa

   BANBANCI FASSARA INDIAN HAUSA (Sultan)


zaki bar min gida yau din nan bana son ganinki, na tsaneki halima tace amma alhaji ai ka bari se gobe in tafi ko tunda dare yayi, ga tsohon ciki, ya zanyi ya kalleta cikin bacin rai, yace miye amfaninki da har zan bari ki kwana a cikin gidana, kamar yanda abincinki da ruwanki ya kare a cikin gidan nan, haka kwananki ya kare a ciki dan haka tashi ki fita, halima tace amma. alhaji. shissh ya daga mata hannu alamun baya son jin komi daga gareta, da kanshi ya dagaka, ya fita da ita tana hawaye, hajia maryam da aka fi sani da mommy ta daga hannu sama, tana mai gode ma Allah tace.

  kai Allah mun gode maka daka rabamu da kaya, a gayas umma ta gaida asha haka ta fita cikin daren nan kusan 11 na dare, ta tunkari titi, tana tafiya gashi ba motan hayan da zata ce ta shiga ya kaita unguwan da take, haka tana tafiya tana hawaye, bata ankara ba, ta fadi a kasa, ga nakuda ya taho mata gadan gadan, haka ta duke a kasan nan, tana murkusu ya Allah kaine abin godiya, kai ka daura min jarabawan nan, Allah ka kawo min agajinka, wani mai mota ya faka motarshi, subhanallahi! hajia lafia? sannu tashi muje asibiti, da kyar ta yunkura da temakonshi ta shiga motan, yaja yayi asibiti da ita , isar su asibiti, aka amsheta da gaggawa, sbd ta fita hayyacinta, bata san wanda ke kanta ba.

Ayshat madu: nakuda ya dauketa, tsawon lokaci, wanda ya kaita har safiya, halima tana abu daya, bata haihu ba, duk tabi ta galabaita, bata san wanda ke kanta ba, doctor ya fito yana neman wanda ya kawota, wata nurse da suke tare, tace mashi ai be riga ya iso ba, yace to in ya iso kice ina son magana dashi, tace ok sis, ya wuce, ba a jima ba, 

   Sai gashi ya iso asibitin, nurse ta fada mashi sakon doctor, yace to ba damuwa, ya shiga office dinshi, ya sameshi, suka gaisa, yace dama abinda yasa nasa kazo, sakamakon nakudar da matarka ta dade tana yi, ya zama dole a mata operation, saboda ba zata iya haihuwa da wuri ba, muna bukatan sa hannunka, dan gaskia za a iya rasa rayukansu, daga ita har baby din dake cikinta yace to ba damuwa, haka yasa hannu, aka shiga da ita thearter room, se fatan Allah ya fito da halimatu lafiya, ita da baby din dake cikinta.

 Ayshat madu: bayan gama mata operation, aka fito da ita, dakin da zata huta,  baby kuma aka shiryata, aka miko ma bawan Allah daya temaka mata, yace har kun fito? tace eh insha Allahu zata farka itama nan bada jimawa ba, yace to shikenan.

sannunku, yace: tunda Allah yasa an gama mata operation a sa'a, zanje in dawo zuwa anjima, ga baby din se ki kula da ita, ta amsheta, shi kuma ya tafi, zuwa yamma halima ta farka, doctor ya shiga ya kara dubata, aka hadata da baby dinta, bayan sallan magriba, se gashi ya shigo ya sameta, kwance ga baby don't a kwance kusa da ita, yasa hannunshi ya dauketa, ya samu kujera, ya zauna, yace mata sannu ya jikin naki? tace da sauki, 

  Yace ai alhadulillah aikin yayi kyau, dan gashi kin samu sosai, sunana alhaji aliyu, dana kawoki nan, tace na gode, Allah yasaka da alkhairi, ya mike ya aje baby din, 
da kanshi ya hada mata tea, ya mika mata, ta amsa tace na gode, ya kara daukan baby din, yace yarinyar nan ta birgeni sosai, ta shiga raina, ina jinta sosai a raina, halima tayi murmushi, tace na gode. bata ankara ba, hawaye ya zubo mata, yace subhanallahi! baiwar Allah lafiya kuwa? tace bakomai, yace a'a akwai saboda hakanan zaki hau kuka? ta kara cewa bakomai, yace to shikenan, ba zan takura maki sai kin fada min ba, yauwa ina ne gidanku? saboda a fada masu su san halin da kike ciki. 

tace ina unguwan dosa ne, ta mishi kwatancen gidansu, yace to insha Allahu zan samu naje zuwa gobe, ko yanzu idan na fita, tace to na gode sosai, yace kada ki damu, bari in samu in tafi ana kiran isha'i, daga can zan wuce gida, se gobe na Kara zuwa, tace Allah ya kaimu, bayan fitan shi, ta kalli baby dinta, hawaye ya kara sauka a fuskanta, tace Allah ka raya min ita, ka tsare min ita daga duk wani sharrin halitta.

Ayshat madu: bayan gama mata operation, aka fito da ita, dakin da zata huta, baby kuma aka shiryata, aka miko ma bawan Allah daya temaka mata,

Post a Comment

Previous Post Next Post