Barayi Fassarar Indian Hausa

   BARAYI 1&2 SABUWAR FASSARA INDIAN HAUSA (Sultan)

Karku manta Zaku iya Kallo Dakuma Saukewa Acikin wayanku dakuma Komfuta Cikin Sauki 👉


Kun Karanta Wannan?

Nan suka hau dudduba kalar kayan da zasu saka, Afnan ce taci karo da wata had`ad`d`iyar top gown hot pink sai torches d`in black kad`an kad`an, baki d`aya k`irjin rigar a bud`e yake da wasu hudojin da aka k`awata su da zanen manyan flowers, bayan rigar yafi gaban ta tsawo da kad`an, hannun ta ma d`aya dogo d`aya gajere ne, gata da shape sosai irin wadda take fidda zahirin coca cola shape na mace, (niko Amrah nace wannan kyan ta masu aure su same ta, ai ranar babu oga ba zuwa office..lol). 
      
Bayan ta tabbatar da rigar ta burge ta ne suka hau dubama Feenat nata, "nidai Afnan pls bana son mai tallan jikin nan, asamar min mai rufe tsiraici" Cikin fushi Afnan tace "wallahi duk wadda aka samu ita zaki d`auka kuma dole ki saka ta",
    
  Shiru Feenat tayi taci gaba da bin bayan Afnan suna kewaye boutique d`in, da k`yar suka samu wata gown ash da torches d`in pink, gown ce ta mutunci mai A shape, zata iya sauka har k`asa, tana da turtle neck da dogon hannu. Sosai Feenat taji dad`in wannan rigar, dan tasan zata iya sakata ba tare da taji komai ba. 
   Side d`in jewelries suka koma, nan naga k`aryar fashion sark`a da `yan kunne da abun hannu, komai na AA BOUTIQUE kyau gare shi, nan Afnan ta zab`i wata siririyar chain mai kyau, Feenat ma irin shi ta zab`a, kud`in suka biya sannan suka koma mota dan nufar gida.

        Cike da damuwa Feenat ta kalli Afnan tace "yanzu Afnan wace k`arya zan ma Ummah anjima idan zan fito?"
"Oho miki, sai kisan abunda zaki fad`a mata, nidai k`arfe biyar na yamma zanzo d`aukar ki, ki tabbatar kin shirya by then",
   Tun daga nan kuma sukayi shiru su duka har akazo k`ofar gidan su Feenat.
    Afnan da kanta ta fitar ma Feenat da kayan ta daga leda, cikin in ina Feenat tace "Afnan ki tafi da kayan nan idan mun tafi can zan saka, dan yanzu Ummah zata iya cewa in bata ta gani kuma nasan halin ta zata iya fahimtar wani abu",
Bata ce mata komai ba sai jinjina kanta da tayi, daga nan taja motar ta sai gida.

      "Momy ta samu fa, yau ma akwai wani casun" Wadda ta kira da momy tayi mirmushi tace "kedai Ruky bakya gajiya da casu, kullun baki nan baki can, duk inda ake wani biki ko party kina can ko? Yau kuma wane casu ne akeyi?"
   
 "Momy birthday party`n Kerry ne fa za`ayi kuma mune best friends nata, idan bamuje ba waye zaije? Momy tace ehh kuma fa gaskiyan ki, to amma ki k`ure kwalliya dan nasan yau akwai wankan gayu, so nake auta ta tafi kowa yin kyau a wurin, kiyi chajin iphone d`in ki sosai yanda zaki d`auko pictures da yawa",
     Can naji wata murya zazzak`a daga bakin k`ofa tana fad`in "haba momy, wai yaushe zaku tuba ga Allah ne ki daina d`ora Ruk`ayya akan wannan munanan halayen? Ku baku ma tsoron mutuwar ku? Koda yaushe fa mutuwa zata iya riskar ku dan ita bata alerting mutun kafin tazo.
    
Cikin takaici momy tace "ke Rumaysa wai ina ruwan ki ne? Ni tunda na gane ke ba wayayyiya bace kinga ina saka ki a irin wannan harkokin ne? tou wallahi kul dinki, kar ki kuma jefo mana wannan shegen bakin naki idan muna maganar mu".

     Rumaysah tayi shiru daga nan bata kuma fad`in komai ba, sai dai kuma har a ranta tana tir da Allawadan halin mahaifiyar ta da k`anwar ta Rukayya, mahaifin su yana kabari amma su suna nan basu ta yi mashi addu`ah sai munanan d`abiu, da wannan tunanin ta shiga d`akin ta cike da tsanar halayyar su.

Post a Comment

Previous Post Next Post