Haduwa Indian Hausa Sultan

   HADUWA FASSARAR  (Sultan)

📺 Kidaure kuyi kokarin kallon video tundaga farko har karshe.

Gaisuwa Gareku mutanen Kasar:

  1. Coté D'ivoire 
  2. Saudia
  3. Libya
  4. Sudan
  5. Algeria
  6. Nigerian
  7. Saudi Arabia


Hausa Novel 1
Manal a zaune take akan dining table ita da Mijinta da yaranta Uku,suna cin Abinci, hankalinta na kan Daddyn Hanif dake cin abincinsa hankalinsa kwance,yanda ma yake cin abincin kasan ba k'aramin dadi abinci yake mishi ba,d'agowa Daddyn Hanif yayi suka had'a ido,suka sakarwa da juna murmushi cewa yayi " aa Momin Hanif kallon yanda nake loma kike ko,?" 
   
   Murmushi tayi tace "ko d'aya mai ka gani,"? Loma ya kai bakinsa yace kallona kike mana tunda zu Dan ke ba abincin kike ci ba sosai,karma kiga laifina Dan abincin yayi dadi sosai dole nayi loma" Daddyn Hanif yace yana k'ara kai loman abinci bakinsa" Hanif d'an shekara takwas dariya ya kwashe dashi yace "daddy kar dai ka k'ware kamar ranan, " kanensa Salem da taufiqa suma dariyar suka yi suna kallon daddyn nasu Dan indai zai ci abinci sai yayi santi, Dan Manal ta iya girki sosai ba laifi,ahaka suka gama cin abincin suna zolayar juna, su Hanif suka tashi suka nufi Palo,suka bar Manal da Yusif a zaune akan dining, sai da Yusif ya tabbatar da yaran sun gama ficewa ya matsa kusa da Manal yace 

"Mom Hanif wanan girkin yafi na koyaushe dadi,idan na dawo dole na biya,badan ina so naje nayiwa Hajiya sallama ba, da babu abinda zai fitar dani."

 tunda ya fara magana take ta zuba murmushi, tace "karka damu daddyn Hanif kayi sauri kaje ka dawo,ina nan na maka tanadi na musamman, Manal tace tana kashe masa ido d'aya murmushin jin d'adi yayi yace " Allah Mom Hanif"

"Allah kuwa kai da zaka yi tafiya gobe kasan dole in tanade ka" janyo ta yayi ya rungumeta yace " bari nayi sauri naje na dawo I can't wait" tare suka mik'e suka nufi Palo, Hanif da Salem na zaune akan kujera suna Home work d'insu,Taufiqa na zaune akasan carpet tana kallo,Yusif wajen su Salem ya nufa ya duba home work d'in da suke yi,ganin sun iya home work d'in ne yasa ya mik'a musu suka cigaba,ya nufi wajen Taufiqa da ta mayar da hankalinta kan kallon da take yi,tsuguna wa yayi a gabanta yace "baby ke kinyi home work d'inki ne"? 

" Nayi Home work d'ina daddy,tun jiya momy ta koya min Murmushi yayi yace "da kyau babyna mai zan taho miki dashi"? 

Da sauri Hanif ya ajiye pencil d'in hanunsa ya nufi inda suke yana " daddy zan raka ka gidan hajiyan" shima Saleem rigima yasa yana zai raka shi,adai dai lokacin da Manal ta fito daga d'akinta hanunta d'auke da wani viva bag, Daddyn Hanif lafiya naga sun sa ka agaba"? 

 Manal tace tana mik'a mishi ledar hanunta tana ya kaiwa Hajiyarsa yace tana gaisheta,k'arbar ledar yayi yana " ki rabani da yaran nan naki sun dage sai sun rakani," 

"Daddyn Hanif ka tafi dasu mana Dan Allah na samu ma nayi barci" Manal tace tana mik'ar da Taufiqa,


"To shikenan kuzo mu tafi,Yusif yace yana yin hanyar waje,Hanif da Salem da sauri suka d'auko takalminsu suka bishi da gudu suna murna,Manal d'akin ta nufa ta d'auko wa Taufiqa Hijabinta ta sa mata,ta rik'e hanunta suka yi waje.

Gaban motar ta bud'e ta sa Taufiqa aciki,Dan su Hanif suna zaune abaya,rufe k'ofar motar tayi ta lek'ar da kanta tace " Daddyn Hanif sai kun dawo Ku gaishe min da hajiyar," amadadin ya bata amsa K'ane mata ido yayi ya faki idon su Saleem ya hura mata kiss,murmushi tayi itama ta mishi blowing Kiss ta ja da baya,yaja motar su Hanif na mata bye bye,tana tsaye har sai da suka bar harabar gidan,ta koma ciki tana murmushi.


Manal da Yusif shekararsu goma sha uku da aure,aure suka yi na soyayya,Inda Allah ya azurta su da yara uku,Hanif shine first born,yana da shekara 8,Salem shine second born yana da 6,sai Taufiqa da take da shekara 4,Yusuf d'an chanji ne yana aiki anan Abuja,duk weekends yake zuwa gida,ran Monday ya koma da sassafe, akwai soyayya mai k'arfi atsakaninsa da Manal duk da dadewar da suka yi da aure hakan bai sa sun rage San da suke wa junansu ba,Dan idan ba saninsu kayi ba,tunani zaka yi basu dade da aure ba Dan yanda suke Ji da juna kamar basu dade da aure ba, Yusuf burinsa a rayuwa bai wuce yaga ya farantawa Manal da 'yayanta ba,duk da yana da kud'i hakan bai sa yayi amfani da wanan damar yayi kula kule 'yan mata ba.
   
     Inda Manal itama nata b'angaren hakane,tana masifar San mijinta sabida yana k'ok'arin faranta mata babu abinda ta nema ta rasa a rayuwarta,sai dai ta godewa Allah,Manal na da Ilimin addinin dai dai gwargwado,yaranta sun taso da tarbiyya da ilimin addinin kwarai da gaske,dan tayi tsayuwar daka wajen koyawa yaranta ilimin addini,shi yasa duk inda yaran suka shiga sai an yaba irin tarbiyar da mahaifiyarsu ta musu,hakan kuwa ba k'aramin farantawa Yusif rai yake ba,shi yasa ya ke k'ara Santa a zuciyarsa.

Post a Comment

Previous Post Next Post