Jami'i Suriya Fassarar Indian Hausa

   JAMI'I SURIYA INDIAN HAUSA 2022  (Sultan)


Gawani Sabon 
Kullum arzikin shariff bunkasa yakeyi  Shi Isah yana neman aiki cos yaga yanashirin talaucewa matarshi Hauwa  mutumiyar kirki  kullum cikin yimai wa'azi take mai cos talura da irin kiyayyar da mijin ta kemawa Dan uwanshi.  Alokacin kuwa sunada yarsu Fatima dakuma sabon ciki . Lokacin da  HAUWA taga talaucin yakusan musu kamun kazar kuku ,saitabada shawarar yaje wajen Shariff tunda yanada shi ,aikuwa anan yake gwada mata babu abinda zaisa shi neman taimako awajen kaninshi ,babu yadda ta iya ,haka tabarshi. 

Lokacin na tafiya arzikin shariff  kara bunkasa yaketayi ,yanxu Kuma Shirin aure yakeyi , sai wata mumunar labari yariske shi wai Fatima da kannuwata (kasancewan mamansu takara haifan wata maiSuna Maryam )Suna wasa da candle bisa ganganci  wutaya  diga a curtain, ahankali yake kamawada wuta, dakyar aka samu aka fitardasu daga cikin gida, ko kwandala ba'a fitar daga cikin gidan bah  kasansewan night neh . Daman ISAH Kuma da certificate yake takama  gashi yanxu ya kone,dolenshi ya amsa tayin matarshi nazuwa wajen Shariff,  batareda bata lokaci bah Shariff yabashi kyautar Wani katon gida daga cikin gidajenshi na  anguwar GIDA DUBU ,dakuma babbar shago wanda shida kanshi yake supplying dinkayan shop din  kasancewan ISAH baxaiya aikin office bah . Aganin Shariff kiyayyar da Isah yakemai zai rabu .

Shariff yayi aurenshi inda lokacinda yatafi India ya hadu dah CHANDRAMUKHI soyayya mai tsabta yashiga tsakanin su . Chandra ita kadai iyayenta suka Haifa Kuma talakawa neh sosai amma dukda hakan suna samun na daily bread . Iyayen sunyi iya kokarinsu naganin Chandra bata auri Shariff bah amman hakan ya gagara cos Chandra cemusu tayi in basu barta ta auri Wanda takeso bah she will elope with him ,babu yadda suka iya aka suka barta.

Anyi aure da wata daya ,Chandra ta musulunta inda tazabi Suna NARGIS cos a India ta musulunta Kuma wai sunan kakanta nawajen amminta neh .NANU (kaka) taji Dadi sosai inda Kuma iyayenta suka yi fushi da ita, dakyar  dai suka sauko kasancewan bakin alkalami ya riga ya bushe.

Aurensu da wata biyu  suka koma Nigeria sunyi kukan rabuwa barinma Nargis da amminta ,dakyar dai suka hakura inda shikuma yamusu alkawarin zasu nah zuwa lokaci zuwa lokaci.

Gidan yayanshi yafara sauka  donya gabatarda matarshi ga yayanshi , gigicewa neh kawai Isah baiyi bah sanda yakalle irin kyan Nargis  atake kuwa yakara tsananta tsanan dayamawa  kaninshi Kuma ya kudurta Wani aniya akansu. Sun tare awani big mansion  nagani nafada a G.R.A  cikin garin Bauchi.

Kwanci tashi babu wiya inda na Hango Nargis da bukekiyar ciki  wanda haihuwa yau ko gobe.  Cikin dare Nargis tafara naquda inda Shariff ya garzaya da ita NI'IMA Consultant  Hospital . Bata Dade dafara naquda bah Allah ya sauke ta lafiya inda ta haife yarinya dagabaya kuma aka gane ba ita kadai bace ,after one hour takara haifo wata ,kuma a haihuwan nabiyun neh tasha wahala. Yanbiyun ta  kyawawan gaske kasancewan Nargis mah ba'a baya bah wajen kyau.

Ranar Suna  yanbiyu sukaci suna HASANA ( NAFHIRA) dakuma HUSAINA(NADHIRA), alokacin Kuma ya'ya Isah  wato  Fatima da maryam Sun girme su .Daganan Kuma haihuwa yatsayawa Nargis  sbd mahaifan ta bashida kwari.


12years later

Abubuwa dayawa sunfaru ciki kuwa shine alfarmanda  Nargis  (momma)taroki mijinta daya Kara aure ,soboda yanda ta lura mijinta (dady)Mai son ya'ya ,dakyar da sudin goshi  ya yarda, inda Kuma yace tanema Mai Mata cos Shi babu wanda yake SO batayi kasa a guiwa bah  tazaba mai  yar ajikinta maiSuna Amatullah .

SU Amatullah talakawane sosai ,lokacin da aka mata maganar auren mijin uwar gidanta taso taki ,saida aka hada da roko kafin ta amince dayake Kuma tana mugun ganin  mutuncin Momma. Aisha irin mutanen nan neh masu saukin kai ,nutsuwa dakuma rike addini ,ita ta raini NAFHI da ABAR SO  tana mugun son yaran Kuma suma Suna son ta ,acikin halayen Momma  da antynsu babu wanda basu dauko bah . Anyi aure lafiya inda bayan yan watanni ciki yabayyana ajikinta ,murna awajen familyn ba'a  magana  alokacin neh suka jeh kasa mai tsarki sauke farilla dukda bawannan bane zuwansu nafarko bah Kuma alokacin suka hadu dah Amin. 

Sun dawo da wata daya  aka nemi dadynsu   aka rasa , sunyi kuka harsun godewa Allah ,bayan yan watanni antynsu  ta haife baby boy inda yaci sunan Salim wanda daman kafin bacewar dadynsu yace sunan yake SO.

Nafhi (haka akecemata) da Nadhira ( ABAR SO KOKUMA BABY,haka sukecemata ) sunje gari ruka da dama Wanda ba'acikin Nigeria bah. NAFHI  tafi ABAR SO  hakuri nesa ba kusa  bah while ita ABAR SO tanada saurin fushi ga shegen zuciya Kuma duk sunada ilimi sosai ,babu abinda basu iya bah .


2 years later

Cikin shekaru biyun da sukawuce anyi zaman Dadi dakuma bah Dadi a familyn. Saikuma labari tariskesu wai ansamu gawan dadynsu,basu yarda da abinda aka fada bah sanda aka kawo gawar dadynsu nan kuwa tashin hankali yadawo Sabuwa a familyn .

Sun fito takaba kenan wata Sabuwa alamari ya bullo wai dadynsu yayi signing din duk will nashi wa yayanshi Isah  wannan batu ya girgiza su ainun ace wai duk propertyn su basuda kaso aciki sai gidan da suke zaune ,ai atake jini...

Post a Comment

Previous Post Next Post