Jan Zaki Fassarar Indian Hausa

   JAN ZAKI FASSARAR INDIAN HAUSA  (Sultan)

 
  Haka zameena ta nufi hanyar gida, tana tunanin zeeyad cikin raita, yace "ya Allah ka kare mu zeeyad, Allah kazamu gatansa,kayi mashi Arzikin mai albarka, sabod tun da zeeyad ya dawo daga youth service bai samu aiki bah ,gashi maraya,ni kadai yake gani yana jin dadi,oh ni zameena.

    Amma gashi Abba ya rabamu,haka de ta cigaba da tafiya tana kuka har ta isa gida,haka zameena ta kasance cikin kuka da bacin rai har zuwa ranar dauri aurenta ,yau ta kama asabar dai dai ranar da aka daura auren zameena da yaya Assad, tayi kuka har tagaji daga baya ta hakura,sbd ba abun da ita Iya.

Abba ya kirata cikin daki yayi mata nasiha da tayiwa yaya Assad biyayya,cikin su yaya Assad aka ware masu daki daya,haka suke cigaba da zama tare da Assad ba dadi ba wahala,saboda ban ta taba fuskan tar wulakanci ba ko rashin kulawa ah gunsa,sun zaman lfy,shiyasa ta rumgumi kadare zama dashi,
    
 Yau auren zameena da Assad wata ukku kenan,Wata rana ta ,tashi da matsanaci zazabi,har ta kasa fitowa gwaggo tashiga dakin tanacewa"zameena duk yau banji kiba ,ko lfy?cikin murya ta maras lfy tace"bana jin dadi ne gwaggo, (Subhanalli)gwaggo tace"haba shine baki fadamu ba,shiru zameena tayi ba tare da tace komai ba,sai gwaggo tace tashi muje asibiti,tashi tayi tasa hijab,suka fita, dayake tun da sukayi aure bata kara fita waje, ba.

   Haka suka tare mai Napep suka nufi asibiti,nan likita yasa akayimata gwaje-gwaje,cikin hour daya aka kawo masu saka mako Wanda yanuna cewa tana dauke da juna biyu na tsawon Wata ukku,gwaggo tayi murna sosai,agefen zameena kuwa ta rasa gani wane hali take ciki murna ko bakin ciki, how she wish it was 4 zeeyad, haka suka dawo gida zameena takasa cewa komai,gwaggo kuwa sai rawar jiki takeyi zata samu jika,magana da aka basu asibiti sune ta ba zameena tare dacewa taji ta kwanta.

 Wajan 6:pm su Abba suka dawo daga kasuwa na gwaggo ta ke shaida masu zameena nada juna biyu murna sosai sukayi tare dayimata addu,ar Allah ya raba lfy,koda Assad ya dawo yasamu wana labarin murna a gunsa bata misaltuwa,kula sosai zameena take samu awajan iyayenta da mijinta,
    Wata ranar tafiya ta kama su Abba zuwa sokoto domin wani kasuwanci tun 7:pm su Abba suka kama hanya,zameena kuwa ta koma daki ta kwanta ,da misalin karfi 4:30pm na yamma Assad ya shigo cikin gida hankalishi atashi yana kiran gwaggo, da gudu gwaggo ta fito don jin meke faruwa ,dai-dai na zameena itama ta fito ,saboda jin murya yaya Assad.
   
 Na Assad yace shikena murasa su Abba yanzu aka kirani ake fadamu sunyi accident kuma motar ta kone,sunyi kuka da juyayin su Abba ,ba kamar zameena da yanzu ta dawo marinya gaba da baya,suna cikin haka ne Assad ya samu aiki ah lagos,suka koma can da zama ,suka bar gwaggo ah kd,gwaggo bata so zameena ta jiba sbd cikin jikinta amma ba yanda ta Iya tunda Assad yayi insisting dole tabare suka wuce tare,time din cikin zameena yana Wata 7, haka suka tafi suka suka ahwata unguwa mai suna Agege.

Post a Comment

Previous Post Next Post