Fada da Aljan Fassarar Sultan Indian Hausa 2022

   FADA DA ALJAN 1&2 (Sultan)

Mungode da kasancewa damu akodayaushe Karkumanta kuyi mana Subscribe.

 Zarah ko ta saki jikinta se wasa take har bata so taji an mata maganar su mommy ranar da zata koma daddy da kanshi yazo daukanta duk ta cika gida da ihunta daddyn kamal ya kirata taje yace zarah baki son komawa tace eh daddy kada ka bari na koma duka gidan mugunta suke min su inna gaje ne kawai suke sona dasu bala amma su mommy da yaranta basu sona har barina da yunwa ake ace abinci ya kare in tafi school banyi breakfast ba tana fada tana hawaye daddy yace zarah ba zan kara bari wani yaci zalinki ba kinga bana 

  Zama a gida tace tunda baka zama a gida ka barni a nan yace kiyi hakuri zan rinka baki kulawa share hawayenki kinji ta goge daddy ya gyara zama yace to alh bashir kaga ya kamata ka rinka jan yarinyar nan a jikinka yace insha Allahu daddy yace zarah ga kayan makaranta ki rinka tafiya dashi ta kalla taga bobo caprisonne da biscuit tace daddy ba zanje dashi gida ba sbd idan naje dashi ba za a rinka bani ba kwacewa zatayi kaga ma duka kayan wasan da ka siya min duka ta amshe taba husna daddy yace ka gani ko Allah ka gyara tsarin gidanka tun kafin nan gaba ya gagareka aunty tace tun yaushe ya gagareshi haka zarah na kuka ya tafi da ita aunty tace ki dena kuka dana dawo makka zanzo na daukeki itama ta wuce daki tana hawaye goggo rabi ta bita tace haba auntyn.

  Yara kiyi hakuri kada kisa damuwa a ranki kizo wata cuta ta shigeki gara ki amshi yarinyarki ko mu sbd sabo da ita mun shiga damuwa ga yara can ma kuka suke ganin kinayi dan Allah kiyi shiru tace goggo rabi ya zanyi tace kawai ki amshi diyarki tace bari mu dawo makka inga yanda za ayi suna isa gida cikin tsoro da sauri ta shiga dakin dan karta hadu da kowa kafin ta ida shiga dakin mommy tace waye da sauri ta C dawo da baya ta duka ta gaidata taki amsawa taci gaba ta daka mata tsawa tace dole sena amsa tashi ki bani waje da sauri ta mike ta bar wurin daddy ko ya kasa ma mommy magana se yayi yunkurin mata mgn seya kasa haka zarah taci gaba da.

    Fuskantar tsangwama da UKUBA daddy ya fita ze koma abuja da sauri zarah ta fita ta sameshi yace zarah ya akayi tace daddy har yanzu daddy da dasu aunty Khadija basu dena min abinda suke ba ko baka ma mommy maganar ba ya shafa kanta cikin tausayawa yace zarah nayi amma idan na dawo zan kara masu mgn kinga yanzu yamma tayi ban tafi da wuri ba tace to har ya shiga mota ta kara tsaidashi yace ya akayi kuma zarah tace daddy bafa a bani abinci idan zanje school wataran m bana ci nake tafiya yaya deen ke kawo min kuma ya tafi makka shima ya dau yan naira hamsin na dubu daya ya bata yace ki boye ki rinka kashe hamsin ko dari tace na gode ta shiga gida shi kuma ya tafi tasa kudin cikin.

   Jakanta a haka ta samu in anyi break take siyan wani abin malama suwaiba ta kirata tace zarah naga kina kashe kudi bade na wani kika dauka ba ko ta girgiza kai tace a'a daddy na ya bani zarah kudi ya kare ta koma gidan jiya haka take zama taci kuka idonta gaba 1 ya jagwale sbd kuka gashi ya hadu da ciwo kuma be samu kula ba tana zaune a jikin bishiya tana kuka malama suwaiba tazo ta sameta tace zarah me kike a nan har an koma class ke kadai ba kowa tace anty yunwa nake ji tun jiya da rana dana ci ban kara ci ba da kanta ta fita wurin me tea ta hado mata mai kauri da kwai da indomie ta kawo mata taci sosai sannan suka koma class wata sabuwa komawarta class ido yace be san da rubutu ba ya rufe ruf.

Post a Comment

Previous Post Next Post