Gabar Gida Sabuwar Fassarar sultan Indian Hausa 2022

   GABAR GIDA (Sultan)

Karkumanta zaku iya Samu Garabasa Fina-Finai guda 2900 Akyauta Dazaran Kinsamu Daman Shiga Tsarinmu na VIP Indian Hausa


Kayataccen

  Yana eje kubewar komawa yai dakin ya samu bakin gado ya zauna snn yace ni dae aisha zantafi. Aisha dake kwance ta tashi zaune snn tace katafi ina? Nasir yace g'idan Fatima mana. 

  Aisha tace g'idan Fatima komawa? 'Haba Yallabai meyasa kakemin h'aka sbd Allah' Idan ba mantuwa nai ba ranar da Hauwa tazo nice fa da girki amma h'aka ka tsanleke kaje g'idan ta ban nuna damuwata ba sbd nasan ba'a tare kukeba na barka katafi g'idan ta har kwana biyu yanxu da yakamata ace ka nan shine zakaje g'idan Fatima kuma bayan nan yakamata ka dawo. 
Gaskiya Yallabai bazan boye maka zan'iya hakuri akan komai amma banda irin wanga abubuwan' sbd Allah kodan kaga ni banida kowa ne a garin nan sae kai yasa kakemin h'aka Aisha tana mgnr ne da fashewa da kuka 😭. 

  murmushi kawai Nasir yai ha'de da jawota jikinshi yana lallashinta yana cewa to ya'isa h'aka Aisha ta Idan banda abinki ni banga abin kuka ba 'k'uma mgnr kice bakida kowa a garin nan sae ni' naji dadin h'aka amma k'uma kada ki mance kinada Allah da manzonsa ga k'uma to ai kece mai gata gaki da Allah da manzonsa ga k'uma ni mijinki da h'aka ke kikafi kowa gata dan h'aka ki dai na damu kanki.

"Shiru Aisha tai tana sauraransa har ya kare' snn yace dan h'aka banaso ki sake irin wanga tunanin kina jina ko? "

  Ni zanfita zanje na duba kwana su Fatima da yara na dawo'dan Allah kada ki shiga ciki sbd bilyaminu zai kawo sako kada yanxu yai ta sallama kina ciki. "Sbd duhun dake d'akin yasa bega kwalla ba' jawota yai jikanshi yaci gaba da aiwatar da nufinsa' duk da juye juyen da takeyi amma be hanashi ba h'akan yasa tashi wiya sosae. 

"Da safe be tsaya bata lokaci gun bresfast ba a tsantsaye yasha ya fita' yana fita taja a hankali tashiga wanka' tana cikin wankan ne i'dan ruwan zafi ya tabi gun wani irin zafi takeji da taga h'aka watsa ruwan kawai tai a jiki ta mike. 

"Ruwan lipton kawai tasha ta kwanta' dama tunda Aisha ta samu ciki bata da wani abincin da yawoci lipton sbd koda taci wani abu baya zama duk dadin sa'Sai lipton din shiyasa duk ranar da Nasir baya g'idan ta bata girki' I'dan ma tayi kadan ne na bilyaminu d'an aikenta. 

"Shiyasa yau tai kwanciyarta sbd ko bilyaminu ma da take girkin d'anshi yau bayanan ruwan zafi ne k'uma akwai a plast' Bayan Nasir ya tashi daga aiki sai da yazo g'idan Aisha sbd suyi sallama yau g'idan Fatima zai koma. 

"Dama kwana bibbiyu sukeyi' Aisha na kwance sukai sallama ya fita h'ade da janyo mata kofa ya rufe'bayan fitarsa ne Aisha ta fashe da kuka sai da tai kuka sosae snn ta mike taje toilet tai alwala tazo ta zauna tafara nafila snn tai sallah. 

"Bayan ta'idar ne ta zauna tana tunanin baya a zuciyar tana cewa Ashe mgnr KARIMA gaskiya ne lokaacin da zan auri Yallabai KARIMA take cewa ke Aisha da kuruciyarki zakije ki shiga cikin mata biyu kece ta uku Aisha' Aisha ki daure ki auri yazed yaro kema yarinya koba komai zaku more kuruciyarku ga k'uma kwanciyar hankali. 

"Wlh Aisha bantaba koye maki komai ba a tsakanina da bbnsu su AMIR lokaacin da zaikara AURE Wlh har cikin ziciyata ji nake kamar idan yafita g'idan karya dawo' har addu'a nakeyi i'dan yafita mota ta bugeshi a dawomin da gawarsa sbd kowa ya raya' amma nasan yanxu Aisha ba lallane ki fahimci abinda nake nufi ba ko kisan halin da nake ciki amma tunda yanxu me mata zaki aura watarana ko bani tare dake sai kintuna da mgn ta Aisha. 


Cigaban Labarin 

"Wani irin ajiyar zuciya Aisha tai h'ade da cewa lalla KARIMA Ashe akwai ranar da zan zauna ina tuna wanga mgn' Yau inda ace saurayi na aure wanda beda mata nasan da nunanan tare yana tayani raino ciki da nan-nan dani amma da yake wanga me iyaline ko'ajikinsa gashi yasan banda lfy k'uma duk wanta laluran dana shiga sanadiyar auransane dani sbd kafin nayi aure bansan irin wanga laluran ba sai yanxu k'uma na rasa meke kawomin irin wanga yawan cututuka h'aka ko asibitine zanje naga likita? ' K'uma naje batare da sani Yallabai ba?'. 

"Duk Aisha na mgnr ne a cikin zuciyar ta' can k'uma tace ba nabari xuwa gobe gani yanxu kuraje zasuyi' idan yaro in Yallabai yazo da fase saena sanar dashi.

"Washe gari da safe Aisha nasa idon Yallabai har tara yai amma bezo ba gani h'aka yasa ta dauki waya ta kirashi ringing din farko ya daga h'ade da sallama be tsaya sun gaisa ba yace Aisha ta dan Allah kiyi hakuri nasan nayi lafi amma kiyafe min kinji. 

Post a Comment

Previous Post Next Post