Gidan Yari Fassarar Sultan Sabuwar Fassarar Indian Hausa 2022

   GIDAN YARI (Sultan)


Hausa Storyline
haka muke kiranta yaro, Doctor yakara dan murmusawa Yace Baba na Asalin sunan ai KHADIJA ne, ko?

   Eh hakane asalin sunanta khadija Abubakar, "yauwa Baba adinga cikamata sunanta yafi, "hakane dannan amma tafi gane Dijan yayi murmushi yace" Meyasa metane Baba? Wlh ciwon cikine yake damunta sannan wani lokaci da daddare sai jikinta yayi zafi kamar wuta kuma tana yawan kukan ciwon kai ga amai komi taci sai tayi amai, yadanyi rubutu sannan yadago ya kalleshi yace "tun yaushe ta fara Baba?, 

"kusan wata kenan tana fama, "wata? Likitan ya fada yana zaro ido "haba Baba wata guda tana ciwo anma ba kukaita asibitiba? " mun kaita wani asibiti can gaba da ruganmu sati d'aya suka sallamemu muka koma gida ba sauki shine muka sake komamusu shine suka turo munan, 

Sai da yagama Rubuce Rubucensa, sannan ya kalleshi duk ya diririce sai zufa yakeyi tun kafin yaye magana Baban ya rigashi, araunane yace" Likita me ke damunta? Zata tashi kuwa?
 Doctor ya gyara zama yace "ka kwantar da hankalinka insha ALLAH zata tashi bansan damuwanba tukun sai ankawo saka makon gwajin sai asan abin yi, daidai lokacin nurse din tashigo ta mika masa result din.

   Bayan yagama dubawa ya jawo takarda yayi rubuce rubucensa ajiki ya mika masa, yace "Baba wannan magungunan za'asayo, yakarba yana Dubawa " a'ina ake sayarwa? Doctor yayi jim "Baba kaikadai kazone bakazo da wani wanda zai sauna da itaba? Ni kadaine Likita ba damuwa zan kula da ita Doctor Yadago ya kalli nurse yace" sister hadashi da cleaner ya nuna masa phermercy Baba kazo da kudi? "Eh nazo da kudi sosai ko nawane zan iya saye. 

Insha ALLAH, "ok to kabi wannan zata hada ka da wanda zai nuna maka wajen da ake saida maganin, tana kaishi ga dawo, tadan rusuna tace "ranka yadade kana da petaint guda biyar da suke da appointment naganinka yau, yadan lumshe ridonsa yabude, yace " bazan samu daman ganinsu ayauba amma kidauki files dinsu ki kaima Doctor Habib yadubasu, tadan juya idonta Doctor bakwai guda daya da yake da bukatan ganinka bazaiyuwu yaga waniba sai kai, ok bani filedinsa naga meye Case dinsa? Saida ya duba shi sannan ya tashi yace" , inaso amai da yarinyannan world yanzunnan yafada yana fita, kai tsaye word din Ya nufa yana duba wasu da yakwantar bayan yadan dubasu yadawo jikin gadon da da'aka kwantar da ita, har yanzu bata cikin hayyacinta, dai dai lokacin baban yashigo da magungunan.

   Drip ya daura mata sannan ya samata magungunan, yajuyo yana cire gloves din hanunsa yana kallon Baba da ya dogare sandansa ya harde kafafunsa ya kurama diyar tashi ido, saida ya wanke hannayensa sannan yafita can sashin Cosmo ya nufa,

  Tunda mama jummai ta hangoshi ta tasi da saurinta tana washe baki don tasan abun nima yasamu, duk lokacin da taga Doctor KB yazo wajen da Duke tasan kakanta ta yanke saka don ba karamin kudi yake bataba ta kula da patient Sannu Doctor tafada dai dai lokacin da ta iso wajensa yadan murmusa cikin girmamawa yace "mama karki gaji Dani don ALLAH wani datijjone yazo da "yarshi, anbata gado kuma shi kadai yazo baizo da kowaba, 

Da saurinta ta katseshi Lah bakomi likita za'a kula dasu yanda yadace ALLAH dai yasakama da khairan irin wannan taimako da kakeyi, Baice komiba yajuya ta rufa masa baya Zaune suka sami Baban yarafka tagumi ya tsura mata ido.

  Doctor KB yace" sannu Baba yadora da zaka iya tafiya yanzu, kaje kayi sallah kahuta ga mama zata cigaba da kula da ita in akwai abun da kake bukata kuma kasanar dani, Baba yadago yana dubanshi yace" bana bukatan komi likita nagode sosai da karramawan da kamin Allah ya maka Albarka, mama jummai ta amsa da Ameen, Doctor KB yajuyo da kallonsa ga nurse ita ma shi take kallo tana mamakin Doctor KB aduk lokacin da wasu daga Kauye sukazo da Mara lfy muddin case din ahanunsa yake sai ya dauki dawainiyansu wasu kamma kacokam din maganin shi zai ke saya yana musu amfani dashi

Sister hadashi da baba Garba yanuna mishi dakin da zai zauna aciki yajuya ba tare da yaji daga garetaba, Kai tsaye office dinshi yanufa bayan yakammala abunda zaiyi yafito ya nufi word anan ya samu Doctorn da zai karbeshi,

Yafara mishi handing over har suka iso kan Dija da zuwa yanxu ta farfado bacci takeyi Doctor na'im yace " wanna yaushe aka Admitting dinta? KB yazura hannayenshi a aljihu yana kallonta 

yace" Da safe aka kawota kuma case dinta serious ne typhoid ne yamata chronicHar yana shirin taba heart dinta ga malaria shima yayi mata munmunan kamu kasan mutanen namu San basa son zuwa asibiti saida ciwo yagama mata illa aka kawota,

 yafada yana shafa sajensa ransa a dagule amatsayinsa na cusaltant Sam baiji dadin ganin result din yarinyanba,

Doctor na'im yagirgiza Kansas cike da takaici yace "ba FULANI bane sam bansan yaushe zasu daina irin wannan haliba, yanzu me yakamata amata? Yajuya yana fita yace" yanzu saidai gobe in Allah yakaimu,

Yana bude motansa ya hango Baba zaune duk hankalinsa yatashi katuwar darduma yadauko abayan motansa yakaraso inda Baban yake agefe ya shinfida masa "yace Baba ga gurin zama nizan tafi gida insha ALLAH zanzo da dare, "likita yaza muyi inkatafi? Yadan murmusa "Baba kanaji da wannan"yar taka gaskiya
" Ayyah Likita mamatace fa awajen, 

Post a Comment

Previous Post Next Post