Jami'an Tsaro Dauke da Bindigu Sun mamaye Ofishin NNPP maiduguri

 Borno - Jami'an tsaro dauke da bindigu da aka zargin yan sanda ne, a safiyar ranar Alhamis sun mamaye sakatariyar jam'iyyar NNPP da ke Maiduguri, Jihar Borno kwanaki kadan kafin kaddamar da ofishin da ke kusa da Abbaganaram. 


Majiyoyi sun ce rikicin ya samo asali ne a ranar Laraba bayan da shugabannin jam'iyyar suka dauki hayar leburori su musu fentin sabuwar sakatariyar, gabanin zuwan dan takarar shugaban kasarsu, Rabiu Kwankwaso don kaddamar da ofishin. 

Amma, wasu da ake zargin yan daba ne daga jam'iyyun hamayya suka kutsa sakateriyar suka lika fastocin yan takarar su a wurare daban-daban a harabar sakateriyar, Vanguard ta rahoto. 

Hakan bai yi wa magoya bayan jam'iyyar ta NNPP dadi ba kuma daga bisani fada ta kaure tsakaninsu.

Ya kara da cewa baya ga rufe sabuwar sakateriyar, yan sandan sun kama shi sun tafi da shi ofishinsu da ke Maiduguri a safiyar yau Alhamis. Dakaci karin bayani .


Post a Comment

Previous Post Next Post