KGF 3 Fassarar Sultan Indian Hausa

   KGF 3 Sabuwar  (Sultan)


Takari

 Fanfom buhole kakeji, Yara ne da matan aure keta diban ruwa a bakin bohol kamar yadda akasaba akowani kauye. Yarinyace yar shekara goma sha daya ke saman karfen tana buga ruwan yan uwanta biyu sunata faman tarawa suna kwashewa gefe. Dahaka har suka gama ciki duk wani kaya da suka zo dashi gurin. Wani dan gidan laka suke shiga da ruwan duk rigan jikin su yajike kunsan duk ruwan yana komawa cikin roban da suke daukan ruwan.

  Randa ne irinta laka suke zuba ruwan aciki duk bakin randan ya fashe , harda faci akaimay da siminti . akwai shukan Iccen shuwaka a,tsaye gefen randan ruwan .

  Inna yar kulu tafito daga cikin dakin lakan da saboda tsufa har ya dan duka kamar zai zube, amma haka yar kulu ke rayuwa acikin dakin tare da yan marayun diyan ta su hudu hafsat fatima mariya sai Abdul wanda suke ce ma datti saboda sunan mahaifin babansu ne akasa ma yaron.

   Kai amma yau hafsi kunyi saurin samun ruwa akan lokaci, hmmm inna aikin san wanan aikin yar gidan kice , fadima . Wlh layin su kuburah taci, tace atabau mun riga su bada ashirin din mu dole aka kyale mu, muka diba aida layi ko kusa damu baizoba. Fadima ce ta fado cikin gidan dawani katon bahon ruwa akanta tana haki ataimaka asauke ta. 

   Inna yar kulu na fada tasauketa, ; haba fadima wanan bahon yafi karfin ki wlh , ai wanan sai ya buda maki gaba, bahon waki, ka dauko ne ? Wlh na Asiya ce na dauko ka kafin diba yazo garesu, Don Allah yar nan kibar daukan roba mai girma kada ciwo yakamaki banda kudin kaiki ko wurin mai agangama balle asibitin gari Dagudu ta koma donta maida roban da ta dauko na ruwa.

  Inna tagama kwasan tuwo taba kowa nashi uku kwanon su guda datti nashi daban sai inna ita kadai tsugunne abakin murhu bisa wani dan guntun kujeran katako , tanayi tana kara masu miya a tasu kwanon.

  Duk talauci da maraicin su yar kulu da yaranta baisa tai masu sakaci da karatun addini ba dana zamani haka suke zuwa karatusu ,babu mai taimaka masu sai Allah sai yar sanar, saida kamun koko da inna takeyi haikan garin ansanta da wanan sanar basai yaranta sunje yawon talla, ba.   Yau ba akaratun boko sungama aikinsu tunda safe suna sauri sutafi makarantar islamiyar su don malam bugunsu yakeyi idan an makara.

  Gefen hayar su ta islamiya su kaga wasu mata su uku a tsaye suna gaisawa , cikin ladabi su hafsat suka gaida matan , suka tafi.

  Kai wanan matar akwai karfin hali ,wlh inji Ramatu daya daga cikin matan da ke tsaye agefen haya wakenan? inji ; Gajiye , yar kulu mana matan marigayi sani mai shago ai yaran tane nan suka wuce mu taki bari kowa yadaukar mata ko guda ne,Wai a cewar ta itace zata tarbiyar da diyanta don haka ko aure taki yi waisai yaran sun girma , sunyi aure da farko har andauki yar babban amma saboda nacin yar kulu kan wai sai yarinya tayi ilimi dole akadawo mata da yar ta , yanzu duk dangin ta sun kyaleta da abinta dama mijin ba,asan asalinshi ba, Itace uwa itace uba.

  Yar kulu tana da tauhidi azuciyar ta yarda da Allah da kuma duk wani kaddaran da yasamay ta , hakan yasa batasa wa,ranta wani kwadayin duniya ba ita dai akullun taga Allah yabasu abinda zasu ci su sha basai ta tara wani abin duniya ba.

  Kwadayinta su samu dan ilimin zaman duniya data lahira, koda sunyi aurene su iya karanta ko yar wasika ce Saidai mutanen kauyen suna dauka wani girman kaine irin nata , ita wacece da zata hana yaranta talla. GAJIYE takasa zama ta kasa tsaye yanzu yar kulun da tasani itace da wa"yan nan yaran haka jari gida ba,asan yadda za,a sarrafa suba tawani nacewa wai ita yara na karatu ba,talle wata sana,a kwarara. 

   Aiko gobe dole in koma kano wurin hajiya in ji yara yan shekara nawa take bukata idan naga da irin su acikin yaran yar kulu tau nikan abin yazo min da sauki wlh basai na shiga yawon bida ba ga abu a gida.

Post a Comment

Previous Post Next Post