Labarai: Ankai Hari A makarantar Yara a Habasha

 Yara na daga cikin wadanda suka mutu bayan wasu hare-hare ta sama da ake zargin rundunar sojin Habasha da kai wa kan wata makaranta renon yara.

  Yara kanana na daga cikin mutum hudu da suka rasa rayukansu a wasu hare-hare ta sama da ake zargin sojojin Habasha da kai wa a kan wata makarantar renon yara da ke Makele na yankin Tigray. Asusun kula da yara kanana na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya tabbatar da labarin harin inda ya yi Allah-wadai da yadda rikicin ke shafar yara kanana. 

Rikici a tsakanin gwamnatin Habasha da Tigray, ya jefa miliyoyi da ke a yankin na Tigray cikin halin kunci na katsewar abubuwan more rayuwa inda aikin isar da agaji ke ci gaba da fuskantar tsaiko.

Post a Comment

Previous Post Next Post