mashekin Soja fassarar Sultan Indian Hausa

   MASHEKIN SOJA  (Sultan)

Gaisuwa Gareku mutanen Kasar


 Tana zaune a tsakar gida tayi kashi a wando haka ta wurgota tsakar gida ta barta kuda na binta se kuka take kamar ranta ze fita khadija ta fito da bulala a hannunta ta fara tsula mata tace yi mana shiru kin cika mana gida da kuka shegiya me bakin hali irin na uwarta taja tsaki ta tafi ta barta a nan khadija itace diyarsu ta farko me shekara 15 se zainab mansir sadiq umar salma se autarta husna itace tsarar khadija asalin alh bashir da mommy yan zaria ne aiki ya ajeshi kaduna haka tasa hannunta a baki tana tsota har barci ya dauketa a nan tsakar gida ga rana gaje ta shigo me aikinsu tace to lafia zarah kike kwance a nan ta dauketa tayi sashin da suke zaune a can ta shiga toilet ta. 
 
 Wanke mata kashin ta mata wanka ta dauko abinci ta fara bata da sauri ta rinka amsa tana ci da taga bata bata da wuri ba tasa hannu da kanta ta diba juma ta kalli gaje tace anya kuwa akwai rikon arziki a tare da hajia kuwa nide na tausaya ma zarah gaje tace nima wllh dan wuyar da zata ci a gidan nan sede Allah ya kawo mata agaji baki nan ai mamanta take zaune gidan nan ba karamin kaskanci tasha ba taci wahala juma tace kai wannan mata ba digon imani a tare da ita haka mommy ta banko dakin tace uban wa ya baku izinin daukarta ku shigo da ita gaje tace ayi hakuri hajia tace duk wanda na. 
  
     Kara ganin ya temaka mata dede yake da barin aiki a gidan nan ta finciko zarah tana kuka ta fita da ita ta direta a kasa ta dauko wasu kayan da pampers ta fara sa mata tana kuka ta kai mata duka a baki tace yimin shiru shegiya bade an kawoki gidan nan ba se inga yanda zaki ji dadi a cikinta ta gama sa mata ta dawo da ita palour aka dankwafar da ita a kasa ta rakube a wuri guda se ajiyar zuciya take husna tana zaune a kan cinyar mamanta ga goran bobo a hannunta dasu chocolate zarah ta bita da kallo mommy ta mata dakuwa ta daka mata tsawan data gigitata kinbi se kallon mutane. 

  kike da idanunki kamar na mujiya kwadayayya ta dukar da kanta kasa zainab ta kwashe da daria tace jibeta se kace munafuka karamar yarinya da ita mommy tace to da miye ita an tsota a wurin muguwar uwa mansir ya tashi ya kai mata rankwashi ta fara kuka aka sata tayi shiru dole oh duniya ina zaki damu yanzu me yarinyar nan ta sani Allah kai mana katangar karfe daga sharrin masu sharri

Post a Comment

Previous Post Next Post