mutum akalla 20 da raunata daruruwa a Iraqi bayan ritayar malamin Shia daga siyasa

 An kashe mutane akalla 20, tare da raunata daruruwa a harabar majalisar dokokin Iraqi sakamakon rikici tsakanin magoya bayan fitaccen malamin Shia din nan Muqtada al-Sadr da jami’an tsaro.

Magoya bayan Muqtada al-Sadr sun mamaye fadar shugaban kasa bayan da jagoran ya sanar da barin siyasa

 A jiya Litinin ne malamin wanda hadakar siyasarsa ta yi nasarar cin kujeru mafiya yawa a zaben majalisar dokokin kasar, ya sanar da yin ritaya daga harkokin siyasa, tare da rufe dukkanin ofisoshinsa abin da ya harzuka magoya bayansa suka je suka mamaye fadar shugaban kasar.

 Daman tun a watan Yuli da Agustan nan magoya bayan malamin suka yi kaka-gida a wajen ginin majalisar dokokin kasar don nuna rashin jin dadinsu da kin kafa sabuwar gwamnati.

 Ana samun rahotanni rikici tsakanin kungiyoyi masu gaba da juna a biranen Basra da Nasiriya da Hillah.

Kamfanonin sufurin jirgin saman a yankin sun dakatar da zira-zirga.

 ‘Yan siyasar kasar da Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Hadakan Musulmi, da Amurka sun yi kira da a kwantar da hankali

Moqtada al-Sadr, malamin Shia mai tsattsauran ra'ayi wanda yake da miliyoyin mabiya, ya sanar da matakin nasa ne a shafin Twitter.

Daruruwan magoya bayan malamin sun yi zaman dirshan a wajen ginin majalisar dokokin kasar ta Iraqi tsawon makonni bayan da tun farko suka mamaye ginin domin nuna kin amincewa da matakin kin kafa sabuwar gwamnatin.

Malamin ya yi sanarwar ne kwana biyu bayan ya yi kira ga dukkanin wadanda ke da alaka ko hannu a siyasar kasar bayan mamayar da Amurka ta yi wa kasar a shekara ta 2003 da su fice daga fagen siyasar

Kawancen siyasarsa ne ya yi nasarar cin yawancin kujerun majaliar dokokin kasar ta Iraqi a babban zaben kasar da aka yi a watan Oktoba na shekarar da ta gabata, sai dai kuma 'yan majalisar bangaren nasa sun yi murabus sakamakon kiki-kaka da aka samu da wani bangaren na Shia da ba sa jituwa a kan wanda za a nada sabon firaminista.

A sanarwar ritayar tasa Al-Sadr a Twitter, ya ce: "Na yanke shawarar daina sa baki a harkokin siyasa, inda a yanzu na sanar da ritayata ta karshe da kuma rufe duk wasu hukumomi [nasa]."

Wasu shafuka na addini da ke da alaka da gwamnatinsa za su ci gaba da kasancewa a bude.

Daga baya kuma kamfanin dillancin labari na Iraq, INA, ya ruwaito cewa malamin ya sanar da shiga yajin cin abinci har sai an kawo karshen tashin hankalin da kuma amfani da makamai.

Sau biyu a kwanan nan magoya bayan Al-Sadr na mamaye majalisa

Sadr, mai shekara 48,ya kasance wani jigo a harkokin jama'a da siyasar tsawon shekara ashirin da ta gabata. 

Dakarunsa na Sojojin Mahdi (Mehdi Army) sun kasnce daya daga cikin kungiyoyin 'yan bindiga, mafiya karfi da suka yaki Amurka da sojojin hadin guiwa na gwamnatin Iraqi bayan mamayar da ta yi sanadiyar ganin bayan gwamnatin Saddam Hussein.

Daga baya ya sauya sunan kungiyar zuwa Rundunar Zaman Lafiya.

(Peace Brigades), kuma ta ci gaba da kasancewa kungiyar mayakan sa-kai, wadda aka yi hadaka da ita wajen kafa rundunar sojin kasar.

Duk da cewa kungiyar 'yan bindigar ta Sojojin Mahdi tana da alaka da Iran, a baya-bayan nan Al-Sadr ya nesanta kansa daga Iran, tare da byyan kansa a matsayin mai kishin kasa da ke son kawo karshen tasirin Amurka da Iran a harkokin cikin gida na Iraqi.

Bangaren siyasa na 'yan Shia wanda ba sa ga maciji da bangaren Al-Sadr din (Coordination Framework) yawanci ya kunshi jam'iyyu ne da ke samun goyon bayan Iran.

Malamin Sadr, wanda ya kasance daya daga cikin fitattun shugabanni, da kusan a kodayaushe yake da bakin rawani da ido baki da sura ta kakkarfa ya samu karbuwa a wajen talakawan Iraqi, wadanda ke fama da rashin aiki da matsalar karancin wutar lantarki da kuma rashawa da ta addabi kasar.

Ya kasance daya daga cikin jiga-jigan kasar da za su iya sa dubban magoya bayansu su fantsama kan tituna a duk lokacin da suka ga dama.

Daruruwan magoya bayan nasa yanzu haka suna can sun yi kaka-gida da zaman dirshan a kofar ginin majalisar dokokin kasar ta Iraqi, tun bayan da suka kusa ginin sau biyu a watan Yuli da kuma wannan na Agusta da ke karewa saboda kiki-kakar siyasar da ake ciki ta kin kafa sabuwar gwamnati.

Post a Comment

Previous Post Next Post