Mutum Bakwai Sun mutu bayan sunci abinci Mai guba a Zamfara Nigeria

 Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta fara bincike kan mutum bakwai ƴan gida daya da suka rasa rayukansu bayan da suka ci abincin da ake zargin akwai guba a ciki.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin ɗin da ta wuce a ƙauyen Danbaza da ke ƙaramar hukumar Maradun.

Bayanai sun ce mutanen sun rasa rayukansu bayan da suka ci dambun da aka yi da dawa a matsayin abincin ranar. Wadanda suka rasa rayukansu sun hada matan aure biyu da yara biyar.

Alhaji Haruna Danbaza wanda shi ne ya rasa iyalinsa bakwai, ya ce uku daga cikin wadanda suka rasa rayukansu matasa ne da suka je aikin gona tare da shi a wannan rana, kuma sun ci abinci bayan sun dawo daga noma.

“Mun dawo daga gona ni da yara samari sai muka iske an yi dambun dawa, matana biyu da ƴan yara duk sun ci.

“Muna shiga gida sai su samarin da muka je gona da su suka ga dambun nan sai suka hau ci su ma har da wawaso, amma ni ban ma kai ga ci ba tukunna.,” in ji magidancin. Alhaji Haruna Danbaza ya ce a cikin dare wasu daga cikin iyainsa nasa suka soma rashin lafiya almarin da ya sa ya garzaya da su asibiti cikin gaggawa. “Marece kuma aka yi tuwo kowa ya ci muka kwanta lafiya lau babu ko mai ciwon kai.

“Ai ƙarfe huɗu na asuba na yi sai ga ɗaya matar tawa ta taso da ɗa a hannu rai a hannun Allah, kan ka ce kwabo sai ga wasu yaran biyu sun sake zubewa, sai kuma ga ɗaya matar tawa ita ma ta zube.“Na garzaya kiran likita kafin na dawo na samu wasu ukun sun sake zubewa. Kafin a yi wani abu har sun fara mutuwa,” ya ce.

Sai dai duk da cewa a hukumance ba a tabbatar da abin da ya yi sanadin mutuwar mutanen ba, amma bayanai sun ce ana tsammanin mutuwar tasu tana da alaƙa da dambun da aka yi da dawar da aka yi wa feshi.

Ko da yake rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta ce tuni ta soma gudanar da bincike a kan al’amarin kamar yadda kakakinta SP Muhammed Shehu ya bayyana. Gwamnatin jihar Zamfara ta nuna ahini akan mutuwar mutanen bakwai. 

A cikin wata sanarwa ta yi kira ga mutane da su riƙa daukar matakan kiyaye wajan dafa abinci musamman waɗanda aka yi wa feshin magani

Post a Comment

Previous Post Next Post