Tawagar Kallon Najeriya Sunkwana a Filin Jirgin kasa a Turkiyya

 Yadda Tawagar Kallon Kafa ta mata ta Nijeriya Suka Kwana a Filin Jirgin kasa Turkiyya.


A wasu hotuna da aka saki a yanar gizo sun nuna yadda maya ƴan wasan Najeriya wato Super Falconets suka yi bacci a kan kujeru wasu a ƙasa a filin jirgin sama na birnin Istanbul na ƙasar Turkiyya a hanyarsu ta komawa gida Najeriya.

Ƙasar Netherlands ce ta fitar da tawagar daga gasar cin kofin duniya ta mata 'yan ƙasa da shekaru 20 ta shekarar 2022 a wasan daf da na kusa da ƙarshe a ranar Lahadi.


Tsohon jami'in yaɗa labarai na Super Eagles, Colin Udoh, wanda ya bayyana hotunan a shafukansa na sada zumunta ya ce, “Ƴan wasan Najeriya mata sun taso daga Costa Rica tun ƙarfe 6:30 na safiyar ranar Litinin.

"Yanzu haka suna Istanbul jirgin su ya tsaya na sa'o'i 24 suna kwance a kan kujeru wasu a ƙasan filin jirgin wasu ma duk inda suka samu."

Daga Hausa Channel

Post a Comment

Previous Post Next Post