Wani Uba yakori Dansa Labarun Duniya Labarun BBC Hausa

 Wani Uba Mai Auri Saki, Yakori dansa daga Gidansa

A yau na haɗu da wannan Wannan yaro mai suna Muhammad, Muhammad dai ya fadan cewa Baban sa ne ya kore shi wai baya sonshi shi da ƴan uwan sa.


Mahaifin yaron dai yana zaune ne a ƙaramar hukumar Tudun Wada ta jihar Kano, a binciken da nai ya nuna cewa mahaifin yaron mutum ne mai Auri saki da yawa.

Shi Wannan yaron ya fadan cewa Baban sa yanada yaya masu yawa a gaban sa, wadanda ya saki mahaifiyar su, a cewar sa da mahaifin nasu yaga suna da yawa, Saiya ɗebe su shi da ƴan uwan sa tare da kai su cikin jeji, inda yace musu kowa ya kama gaban sa.

Yaron yace tun da mahaifin nasu ya kora su jeji bai san inda ƴan uwan sa sukai ba, a yanzu haka yaron yana ta yawo ne daga wancan gari zuwa wancan cikin kaskanci kasancewar baban su ya kore su.

Yaron da bai fi shekara 8 a duniya ba, yace shi kadai ne bai nisa da garin baban su ba, amma yace duk lokacin da yaje gida matar babansu bata bashi abinci idan babansu yazo ya ganshi korar sa yake yace ya bar garin ai yace baya son su.

A yanzu haka wannan yaron ko kayan sawa bashi da shi, sai ɗaya, ya rasa inda zaiyi kamar bashi da iyaye, yace wani garin idan yaje sai an wulaƙanta shi, wani garin kuma su rike shi da kyau, haka yake ta yi tsawon shekara guda, yace shi yana Son a kai shi koda makarantar Allo, domin ya daina wannan yawon.

Bayanin da wannan yaro ya bani ya sani matuƙar mamaki ganin yana ɗan halak amma mahaifin sa ya kore su,? Lallai wasu iyayen ba su da adalci, bai kamata ka dauki Danka na sunna ka jefar dashi ba bakasan gaba mai zai zama ba.

Allah ya kyauta yasa mu dace

Post a Comment

Previous Post Next Post