Fagen Daga Sabuwar fassarar Indian Hausa fassarar sultan

   FAGEN DAGA (Sultan)


Muna godiya da kasancewa damu akodayaushe Karkumanta Kamar kullum mukan turoda Sauke Anan 🌸 Na fassarar Indian Hausa Acikin Channel din Mai Suna Hausa Channel1.

Alkawarinmu na Turo da Addreshin yanar gizo na Samun Daman dauko Sabbin fassarar Indian Hausa film 2022 👉Muna nan Muna kokartawa, Kuma Muna Miko dinbin gaisuwa Mai tarin yawa zuwa wajenku.


Latest Novel

 To my surprise likitan da yake duba Inna ne tsaye a bakin kofan kuma da alama duk yaji maganata, a hankali can kasan makoshin sa yayi magana kaman bayaso yayi sallama ya tako cikin takunsa ta kasaita kamar wani basarake ya tsaya bakin gadon Inna ta ya duka ya dauko statement of result na jikin gadon Inna yana dubawa yana dan rubuce rubucensa gami da duba inna , ni dai ina tsaye ina kallon sa duk haushi da takaicin sa ya cikani fam wallahi.

 A raina nace wannan dai bai dace da Likita ba kyansa land Army amma mutum kullum fuska a daure kamar ta shanu ba fara'a ko na sisin kwabo gashi in zaiyi magana kamar bai so, ni don dole ma nake kallon sa don da ina da iko da na canza wani likitan yana duba innan. maganansa ce ta dawo dani daga zancen zucin da nakeyi wanda naji maganan tun daga tsakar kaina har izuwa babban yatsan kafata, yace "zan bayar da wasu takaddu a waje sai kije ki karba kije ki biya saboda jibi ne aikin" yana maganan kansa akan papers hannun sa, a raina nace "kaji dan rainin hankali wai inje waje, to waje ina? Kuma wajen waye? Na daure kuma na danne zuciyata nace masa "wajen ina zanje? Ya sunkuya yana maida takaddun ma'ajiyan su kamar ba zaiyi magana ba sai da ya gama mayaswa sannan ya daga dara daran idanunsa ya saka cikin nawa ya sarke su nan take naji wani shock na yawo a jiki na kaman electricity da sauri na dauke kaina gefe, yace 

  Nurses station zaki je, ya juya zai fita na dan daga murya nace, wajen waye kuma inji waye? Bai waiwayo ba kuma bai fasa tafiyan ba kuma baiyi magana ba sai da ya kai bakin kofa yace 'duk wanda kika gani kice Dr. JAMAL ne ya aiko ki kawai' sannan ya bude kofan zai fita ya juyo ya nunoni da yatsansa 'yar manuniya yace "yanzu" ya fice.... Sororo nayi kaman wata wawiya na turo dan karamin bakina nace sunan na shi ba dadi kamar sunan yara har yake wani rowarsa, ban bata lokaci ba na dauko purse dina na fita.

     Kamar yanda ya fada min naje nurses station na gaya musu yanda ya gaya min na wuce billing office na biya kudin aikin innata naira dubu tamanin da uku cif nace wannan dole naje bank anjima don kudin saura dubu uku, ni dai fata na da burina Allah ya baiwa Inna lafiya, a gurguje na koma dakin da muke na canza kaya na zuwa dogan riga orange color nayi rolling da dan karamin mayafinsa shima orange banyi wani fenti a fuskata ba sai dan powder da na murza na shafa man baki sai na fito sak kamar wata balarabiyan Morocco.

  Duk da ma ba wani haske gareni ba don nafi dacewa da akirani wankan tarwada niba fara ba kuma ni ba baka ba irin bakin 'yan ethophia ne dani amma akwai kyau, na dauki pause dina na karasa bakin gadon inna na riko hannun ta nace 'inna zanje bank na dawo yanzu bazan dade ba don kudin mu ya kare kinji? Nasan ba ansa min zatayi ba amma nasan tana jina na cika hannun na fice, hadari na gani ya hadu sosai "nace Allah yasa kar ruwa ya sauko har na dawo, na fita na samu mai adaidaita ya kaini baking first bank ina zuwa naga mutum biyu ne kawai a bakin ATM machine din nace Alhamdulillah na karasa na jira suka cire nima na cire kamar jira ruwan yake na na gama ya sauko, aiko ruwa ya kece kamar da bakin kwarya.

   Nan na tsaya karkashin rumfan ATM machine din ina Allah Allah ruwan ya tsaya na samu na koma asibintin kar Inna taji shiru kuma gashi zan bata magani ........ kusan minti talatin ruwan bai tsagaita ba kawai na yanke shawaran fara tafiya da kafa har na samu abin hawa, nayi tafiya sosai amma ban sami abin hawa ba gashi duk na jike shrkaf,can wata mota tazo ta gifta naga tayo reverse kuma ta tsaya kusa dani aka bude kofan mai zaman banza, a raina nace waye wannan ya tare min hanya kuma? Ji nayi kaman daga sama ance ki shigo please kar ruwa ya jika min cikin mota ko na tafi, ga mamakina Dr.Jamal ne fuskan nan a hade kamar wadda akace dole sai ya dauke ni, bani da option dole na bishi gashi duk ruwa yayi min duka sai rawar sanyi nakeyi sai nake jin kamar zazzabi ne ma zai rufe ni, a haka na fada motan ya ja muka cilla kan titi, Wani irin kamashi motan yakeyi gashi ya hadu da da wannan kamshin perfume din nasa mai bala'in dadi ga wani cool music na tashi ga kuma sanyin AC da ya kara saka min zazzabi.

  Sauka yayi gefen titi ya ciro thick coat nashi da yake rataye jikin hanger a bayan motan ya rufa min sannan ya Kashe Ac ya tada motan muka cigaba da tafiya duk mamaki ya cikani, a raina nace dama yana da kirki haka? kodai dan Likita ne yasan illar sanyi da nake ji ne? Ban gama tunanin ba naji yace " in mutum yana da patient baya fita yawo sannan kuma ya dinga duba yanayi garin kafin a fice yawon" uhmm nagode nace dashi kawai.  

  Ba wanda ya sake magana har muka iso TH yana parking na fara kokarin cire coat dinshi na bashi ya bude murfin motan zai fita tare da cewa ki barshi don ni bana saka kayan da mata suka saka ya fice yace "in kin fito ki rufe min mota na, duk na daskare a gurin kamar gunki, to ni mai zanyi da coat dinnan? Na ja numfashi na sauke ajiyan zuciya na shaki daddadan kamshin jikin coat din sannan nayi sauri na cire na ajiye masa akan kujeran nayi sauri na fito kar ya dawo ya sameni cikin motarsa, na rufe Motan nayi gaba.

Post a Comment

Previous Post Next Post