Fusata Sabuwar fassarar sultan Indiyan Hausa 2022

   FUSATA 1&2 (Sultan)


Labarina

  Eh ina sane, to yaushe zan zo kabari na fara fadama umma sai na fadama sanda zaka zo tom shikke na asa da wuri kar aja lokaci dan na tsagu naga kyakkyawar fuskar ki me ciki da murshin da Ke sani fari ciki..hmm tom zan fada mata in ta dawo dg wajen aiki sai ki turo min da address din kamin lkcn tom, mukai sallama tare da daukin ganin junanan mu,umma na ma aiki ciyar gwamnati ce,kamar yanda abbana yake tsohon director a bangare ma'aikatar ilimi dake kano.

    Umma yau fa Ahmad zai zo,to mufeeda kinsan dai dokar gidan nan,bnda kwashe kwashe kisan irin samarin da zaki dinga kulawa,samarin yanxu sai addu'a sabida ba kowanne ne na Allah ba to umma.

   Salamu alaikum wai ana sallama da mufeeda kinji a kace gata nan,fadilah kai shi dakin baki kamin na karasa,ta fito dg daki sanye take da wata hadaddiyar atmafa pink dinki ya amshi jikin dan dama mufeeda ba daga nan ba wajen iya kwalliya ga sarrafa dan kwali ta yafa orange din mayafi da plate shoe ma orange Wanda ya dai dai da ratsin dake jikin atamfar kai masha Allah, ta feshe kanta da turaruka masu dadi kamshi ta karewa kanta kallo a mirror din dakin ita. Kanta Tasan tai kyau.
Umma bari naje tom ki kiyaye kan ki tom dai dai bakin kofar baki ta tsaya can sakamakon daddadan kamshin turaren sa Wanda yasa gabanta yafara faduwa kamar ta koma,ki shigo mana ko baki farin ciki.

     Zaunawa tai cike da kunya ta shiga kanta a kasa tare da sallama,cikin muryar sa me dadi ya amsa,zama tai cikin sanyi jiki kamar wadda kwai ya fashe wa a ciki,sweet sis yau dai na ganki duk da nasha ganin k a pics amma kin fi kyau a zahiri,tana dago kanta suka hada ido dashi cikin kunya ta maida kanta kasa haba sis yau nazo muyi magana mai muhimmanci amma kin ki ki magana.

   Uhmmm ina jinka a gaskiya mufeeda tun sanda na ganki naji kin kwanta min a raina kuma tun lkc nake son ki na bar maganar ne sbd na bari sai kin karasa skul dam gaban ta ya fadi ciki razani tadago kanta da sauri tana kallon sa maimaita maganar ta kana sona yes mufeeda ko baza ki soni ba,ko ban can canci hakan ba pls mufeeda wllh ina sonki ki taimakan dasauri ta tashi ta bar dakin dan gaba daya ita tsoron soyayya take dn gani take kamar wahalace kiranta yake amma har tashige cikin gida ya zauna yana tunani har yaga dai ba zata dawo ba ya tashi ya fita yana fita yaci karo da fadila kanwata ga wannan ki kaiwa auntyn taki tom,da sauri ta shige daki sharaf ta fada gado hade da rintse idanuwa maganganun sa suna dada yimata yawo a kanta mufeeda ina sonki tun ran da muka hadu nake son ki ki taimakn. Aunty wai gashi inji bakon da ya tafi ajiye a nan,waya na nai saurin dauka na kashe dan gaba daya tsoron sa ma nake.

   Gaba daya taka sa sukuni haka ta zauna a daki kamar mara lpy, juyi take a gado dan ta kasa bacci zuciyar ta da tunani kala kala Ahmad daie kyau ne,yana da kyau da duk wata mace zata so sukance tare,kuma yana da nutsuwa wannan tunanin bacci yai awon gaba da ita.

  Shi kuwa Ahmad ya kasa samun nutsuwa sai kai komo ya Ke shi kadai yasan abinda yake Ji game da son yarinyar gaba daya ta sanja mai tunani saima da ya ganta a zahiri kuma trying number dinta yai still akashe tun da ya dawo yake kira amma a kashe,shi kan sa be san iya adadin messages din da ya tura mata ba. Alwala yayi tare da sallah yana rokon Allah yasa mufeedan sa ta so shi. Yana zaune dan yanda yaga rna haka yaga dare,har akai sallar asuba yana abu daya.

Tana idar da sallan asuba ta kunna wayar,messages ne suka fara shigowa,daukan wayar sa yai ya dannan kiran ta da tunanin Allah yasa ta kunna cikin sa'a wayar ya shiga be san sanda ya saki wata nannuyar ajiyar xuciya game da sallam.

Post a Comment

Previous Post Next Post