Gidan Yari Fassarar Sultan Sabuwar fassara Indian Hausa 2022

   GIDAN YARI (Sultan)


Masarautar Jordan
 Kura mata ido yayi, sannan yace. Tabbas Kinyi gaskiya kuma Mahaifiyarta tayi gaskiya da tace Allah sai yabi mata hakkin Yarta da muka zalunta, Ammyn kece kike cewa SAFINAH taki jin maganar iyayenta bayan kece kika daurata akan wannan hanyar, kece kika nuna mata komai tayi dai dai ne, yau gashi kina kiranta sunan mara jin magana, nayi Imani da Allah SAFINAH bazata tana kashe abinda ta haifa ba, dan koni da nake Ubansu bazan nuna mata kaunarsu ba, shine kike tunanin zata kashe Yaranta Ammyna yarinyar da tasha wahalar rayuwa saboda suce zata saka musu guba, wai meye nayi haka na hadu da uwa Mara Adalci irin tabbas ke baki min Adalci ba shine kike tunanin itama bazatawa Yaranta ba.

  Amma ai kasan dole yaran ma su mutu tun da shegune, meye naka makin zafin dan a rage mata nauyin wulakancin da zata fuskanta. Sake baki yayi yana kallon ta cike da mamaki, sannan ya mai maita kalmar da ta furta. Amma kasan dole yaran su mutu? Meye naka na ɗaukar zafi tunda shegune nauyi aka rage mata Kamar wanda aka make take lokacin da likitan nan da ya amshi apple a hannun Ablah ya dawo mishi, sai bayanin da Dr Fu'ad yayi mishi.
*Yaran an ciyar dasu guba ne? Sannan itama me nakudar guba aka bata, sai dai bata ci sosai ba dan babu abinda ya same yaron cikinta.

  Kallon Nannah tayi sannan saka ya fita, har ya isa bakin kofa yace.
"Da hannunki a kashe min Yarana? Da Hannunki A ciwon Natashah? Ammyn na barki da Allah, Ammyn na bar muku Mulkin dan na ajiye, bazan muku hukuncin ba, amma Allah da kanshi zai hukunta ku. Komawa cikin gidan yayi ya kuma diban abinda zai diba, sannan ya je ya saka a mota, daga nan gidan yarin ya wucce yasa aka fidda Bilal, ya mika mishi dukiyar shi, sannan yace.

Daga Ni har kai dole mu hakura da Mulkin jordan domin yafi ƙarfin mu, matukar kace zaka yi sai ka rasa wani abu me daraja naka, kaje Sandia da Ummanshi suna jiranka, nima na bar barwa Ammar mulkin dan naga Adalci a cikin idanunshi. Rungume juna suka yi sannan Bilal yace. Zan koma inda muka fito ne, Moscow ko zamu koma tare, sai mu sayi gida a can Murmushi Ashraf yayi sannan yace.
"Toh haka ma duk shawara ce, ka saya mana babba wanda zamu zauna da jama'ata dan akwai abokaina biyu. Ai idan ma da duk jordan nan ina tabbatarwa da Sarkin Jordan da yayi murabus sabida mace"
        
Murmushi yayi kawai sannan yace.
"Muje Haka suka jera har cikin masarautar, inda ya same Ghaniyu da Fahad sun had'a kan jama'an padar, shiga suka yi sannan ya nemi guri ya zauna.

 Shiru yayi kafin ya mik'e yace.
Natara kune dan ku fahimci abinda nake son nayi, Yau 24-5-2018 Ni Muhammad Ashraf bini Abdullahi bini Yasir na ajiye. Shiru padar yayi sakamakon nauyin abinda zai fada, sannan ya cigaba da cewa. Na ajiye mulkin jordan baki d'ayan,. Na bawa Ammar bini Abu Zarri.

      Toh fa ga Ashraf ya ajiye mulki, wata fata kuke mishi. Ina me baku hakuri abinsa murabus din da nay, Ni kaina bani da yadda na iya ne.  Muryan shine ya kama rawa, sannan ya d'ago kai ya kalle su sannan yace. Na rasa mata na biyu da yarana, don Allah ku manta na zama wani abu a cikin masarautar nan, don Allah karku nime dan yin haka zai sanya Ni a damuwam, Insha Allah! Ashraf bazamu tab'a damunka ba, sai dai idan kujeran taki wanda aka bawa dole zamu nimeka tunda kana kuma raye, bawai ka mutu ba, ban ji dad'in abinda ya faru ba, amma Allah yasa haka shine mafi alkhairi."

          Jingina kai yayi sannan ya mika musu takardan, murabus ya juya gurin Ammar ya mika mishi hannu yace.
"Ina taya ka murna! Allah ya tayaka riko."

   Jingina kai Ammar yayi, yana zubda kwalla saboda tashin hankali dake cikin mulki, masifa ce idan baka bida  ita yadda ya dace ba sai ta kaika ga hallaka.  Godiya da ban hakuri yayi musu sannan ya bar cikin padar, tausayin Mahaifiyarshi yake ji sabida shi ta wurga kanta cikin wannan matsalar, sai dai bazai tafi da ita ko ina ba, Oman yake son fara zuwa yaga halin da Natashah take ciki, kafin ya diro naija. A hankali yake tafiya suna bin bayan shi har inda Ghani ya ajiye motarshi, sannan suka bar Masarautar.

Post a Comment

Previous Post Next Post