Kwaron Wake Sabuwar fassarar sultan Indiyan Hausa 2022

   KWARON WAKE (Sultan)Maaikaciyar Gobnati
   Babansu abdurrahman saddiq dan asalin kasar libiya ne,balaraben libiya a can wani kauye a yankinsu,ruwan sama aka musu mai matukar yawa Wanda ya haddasa ambaliyar ruwa a yankin,da kyar aka samu aka ceci mutane ba Sufi 10 ba,wasu kuma mutum biyar suka taimakawa Kansu da rakuminsu suka yo hanyar Nigeria,su kwana su tashi a sahara har Allah ya kawosu Nigeria,har suka sauka a jigawa state da rakumansu, maza ne su biyar,haka suke fadi tashi a kauyukan jigawa,ciki harda abdurrahman saddiq babansu iklas kenan,ana haka har mutum biyu suka rasu suka rage saura 3,sauran biyu suka koma libiyansu suka bar abdurrahman a Nigeria,yasha wuya yasha talauci a kauyuka,har ya fara Aron gona yana noma,da haka yaci gaba har ya fara samun kudi,ya mallaki gonaki, a wani kauye dake cikin roni nan ya hadu da abu bafulatana wato Babar su iklas,kishiyar babar abu ce ke gallaza mata kasancewar kafin Baban abu ya rasu sun rabu da babarta,shi yasa ya kwace yarsa abu ya bawa matarsa riko.

   Nan abdurrahman ya fada sonta ya tausaya mata,da haka ya dage saida aka aura masa abu,bayan aurensu arzikin abdurrahma ya shahara ga kauyen ana masa sharri dan mafiya,haka abu ta haifi iklas wacce sak babanta ta kwaso,daga nan ya kwashesu suka koma abuja da zama tare da Babar abu wato hajia asmau,wacce yanzu suke hannunta kenan,suke kiranta da ummi tun tasowarsu sukaji mamansu da abbansu suna kiranta ummi shi yasa suka saba suma.har yau suke ce mata ummi,

   Abdurrahman sai da ya mallaki gida a abuja ga har noma ta haka ya biya musu aikin hajji sannan ya ziyarci kasarsa ya nunawa matarsa yan uwansa maza guda biyu da suka rage a duniya,haka gaj asmai ummi kenan,duk ya hada musu hanyar da ko sabo da halin rayuwa zasu iya Neman yan uwansa,

    Bayan suhaila Nada shekara 7 da haihuwa abu maman su iklas da mijinta abdurrahman Baban su iklas suna hanyar dawowarsu daga jigawa zuwa abuja suka tafka hatsari inda Allah yayi musu rasuwa,dukansu,anyi jaje da jimami,yayinda kakarsu ummi ta kira yan uwansa ta sanar musu,har Nigeria sunzo,kuma sun bawa su iklas nasu gudunmuwar,dan suma ba yan uwansa na jini bane,dangi ne kawai sama sama shi yasa basu dauki su iklas ba suka koma kasarsu,

       Ummi kakarsu iklas ce taci gaba da kula dasu,tana sana'ar saida kayan miya,irin su citta,maggi,manja,wake,barkono etc,har abincinsu ya kare,kudin hannunsu ya kare,komai nasu ya kare kat hattana kudin makarantar su babu,lokacin iklas tana ss1,suhaila na primary 2,da haka suka yanke shawarar saida gidan da suke ciki,haka suka siyar da gidan Ganin matane yasa aka cucesu sosai aka siyi gidan arahar banza.

Da haka suka tashi suka koma wajen abuja gidajen dake kusa da garin abuja kafin a karasa cikin city,anan suka sayi wannan gidan da suke ciki,an musu tsada sosai anan kudin ya kusa karewa,shi yasa suka ebo wasu kayan na gidansu da suka siyar Wanda zasu iya amfani dasu suka zuba a gidan da suka siya.

  Sun biyawa suhaila kudin makaranta tun daga primary 2 zuwa jss3 gudun kar a sami matsala,abinci suka jibge komai da suke bukata sai da sukayi dai dai kudinsu,har da jarin kwai da apple,ita kuma ummi takeyin sana'ar siyar da kayan miyarta a gida.

  Islamiyya ma sun biya kudinta na shekaru,iklas ma an canja schl me saukin kudi,ta biya daga jss2 har zuwa ss3.ga saida apple da egg,tana dawowa daga schl zata wuce tallanta, zuwa 4 su tafi islamiyya,haka suke rayuwa har yanzu sun kwashe 2yrs. Yanzu komai ya dagule musu,da tallan da iklas ke zuwa da sana'ar kakarsu ummi suke ci suna sha,da sauran abubuwan rayuwa Wanda ya zama dole.

     Iklas bata da burin da ya wuce tayi karatu me zurfi tayi aikin gomnati dan ta tallafawa kanwarta da ummi,bata da burin da ya wuce tayi aikin goMnati,gashi aikin gomnati na burgeta, ita ko me aikin gomnati ta gani a titi to birgeta takeyi,ko ji tayi ma'aikata na labarin wajen aikinsu to sai ta tsaya ta saurara.

     In tana tuno aikin gomnati ita kadai zaka ga tana daria,idan kana so kaga dariarta ko jin dadinta to ka mata adduar Allah sa ki zama ma'aikaciyar gomnati ko ta company,dan haka duk layinsu in ta wuce ko abokanan tallanta zakaji ana gomnati gomnati wasu suce ma'aikaciya,arnan ko gwarawa da marasa jin Hausa da suka Santa sai kaji suna kiranta the manager.murmushi take musu sosai,

  Indai kana so a nuna ma gidan su iklas to kace gidan su gomnati ko ma'aikaciya, ko gidansu manager. Ya halayen iklas sukene.

Post a Comment

Previous Post Next Post