Mai Nazari Fassarar Sultan Indiyan Hausa 2022

   MAI NAZARI 1&2 (Sultan)Shagali

kam bala'i ta fada yayin da taga motar na kokarin shigewa alamar ma na ciki besan me yayi ba giginyar dake hannunta ta dauka ta saita glass din motar ta wurga cikin sa'a kuwa ta daki glass din side driver sannan taje ta hada da bakin habeeb wanda yagama amsawa da ameen yanzu.

  Wani wawan birki ya taka tare da kiran ya Allah sbd ganin abun da yayi kamar a mafarki dubansa yakai inda habeeb yake yaga nan da nan bakinsa ya haye ya wani kumbura kamar bakin jaba ga kuma jini na zuba yaso yayi dariya harga Allah amma ba hali dole ya ambaci kalmar subahanallah ya fara kokarin bude motar ya fito danya zagaya gurin habeeb dan shi har yanzu baisan ta inda abin yafaru ba amma dai kawai yaga wulgawar abu.

  Tsaye take ta rike kugu da hannu daya dayan kuma wata katuwar giginyar ce datafi ta farko girma 
kwalliyar fuskarta kawai yagani yaji gabansa ya fadi dan wlh babu tantama wannan aljana ce.

    Wa'innahu sulaimanu wa'innahu bismillahir rahmanir raheem ya fara ambata cike da tsoro da faduwar gaba domin dai babu tantama wannan aljana ce duba da yanayin ta gata fara sol saika ce zabiya ga kuma uban bakin kwalli data shafa a bakin nan kamar 'yar auta ga jagira cinku ta hade da kwallin dataja hawayen masoyi.

jikinsa ne ya hau kyarma inda ita kuma dije take ta fahimci meyake nufi aikuwa a zuciyarta tace anzo gurin.

    Harara taci gaba da wurga masa tanata juya ido inda shikuma hakan ke kara firgita shi cikin karkarwar jiki ya qarasa inda habeeb yake ya sunkuyar da kansa kasa sakamakon nauyin daya yi masa sbd giginyar ta bugi kansa ga haqorinsa guda daya daya fita ga bakin ya kumbura yayi tsayi kamar shantu cikin rawar jiki Nasir yakarasa inda yake ya bude murfin motar yana me karanta duk addu'ar data zo bakinsa dago kansa yayi ya dubeshi jin yanata kwarara addu'a sai ya fahimci lallai gamo sukayi domin ya hango aljanar tsaye da irin tasu giginyar ta Aljanu tanata juya ido duk da jirin dayake ji hakan bai hanashi rudewa ba shima ya kama kokarin fitowar nan suka kankame juna shida nasir wanda har kwalla yafara yi dan tsoro musamman duba da yayi da yanayin gurin babu komai sai tarin bishiyoyi da besan kona meye ba amma dai yasan harda na kuka kuma sune gidan aljanu.

Post a Comment

Previous Post Next Post