Masanin Doka Sabuwar fassarar Sultan Indian Hausa film 2022

   MASANIN DOKA 1&2 (Sultan)

Abun Mamaki

  Tana cikin ɗaki ta na gugar uniform ɗinta ta mayar da hankalinta akan gugar bata Ankara ba ta ji a na ta famar rafka sallama a kofar ɗakin, yes shigo abinda ta fada kenan batare da dago kai takalli kofar ba. Farida ce ta shigo ɗakin ɗaure da fuska ta na cewa "Amma gaskiya ba ki da mutunci meerah, Meerah ta ɗan yi murmushi ta ce "Meyafaru kuma besty?

  Farida tace "Tun ɗazu na ke famar rafka sallama ashe ki na ji na ki ka yi banza da ni. Yi hakuri bestyna ban ji bane ke kin san ban isa na kyale ki ba meerah ta faɗa tare da kamo hannun faridar ta zaunar da ita,yanzu dai ba wannan ba meye labari? Meerah ta tambaya. Farida ta ce "Wane irin labari? Habah besty! wane labari zan tambaye ki banda labarin mutumin,uncle wai? Cewar farida,ah! ya na nan ƙlau amma meyasa duk sanda muka haɗu sai kin yi zancensa,ko dai ki na son shi ne ƙawata? Meerah ta sha mur kamar da gaske ta ce "Haba besty! daga tambaya sai ki min wata fassarar ko kin manta cewa saurayin Meenah ne kuma Wanda zai aure ta?.

    Kuma in haka ne ina zan kai uncle manish ɗina? ke manta da zancen muje ki gaida Ammi ko kun gaisa ne? Meerah ta fada tare da riƙo hannun Farida ta tayar da ita tsaye farida ta ce "mu je na gaida ta. Suka bar ɗakin su ka nufi ɗakin Ammi,

Ammi na zaune ta na kallon TV su ka shigo ɗakin da sallama ammi ta amsa da fara'arta ta gaida ta ammi ta amsa tare da cewa ya mamanki ta na lafiya?ki gaidata,

Za ta ji sai anjima ammi ni zan tafi farida ta faɗa,ammi ta ce "Ki gaida gida. Meerah ta rakota har ƙofar gida ta ce "zan shigo anjima idan na dawo daga islamiyya,farida ta ce Allah yasa idan kuma ba ki zo ba wataƙil sai in mun haɗu gobe za mu je school bye,farida ta faɗa. Meerah ta koma ciki Farida ta wuce gida.

 kuwa a ka yi bayan ta dawo islamiyya ta je gidan su Farida da ya ke maƙotansu ne gida biyar ne tsakanin su da gidan su Faridar. Da safe su ka haɗu su ka wuce school

  Class ɗinsu ɗaya su na ss3 ne. Wacece Meerah? Cikaccen sunanta shine Ameerah Usman Lema haifaffiyar garin sokoto ce amma mahaifinta Dan Asalin jihar kano ne.  Ya na zaune ne agarin sokoto shi da iyalansa a nan ya ke kasuwancinsa. Matarsa ɗaya hajiya Karima wadda su ke kira da Ammi. 

Ƴaƴansu uku kacal, biyu maza su ne manya Arif da Adil sai auta Ameerah wadda ta kasance ita kaɗai ce mace a gurinsu su na kiranta da Meerah su na matuƙar ƙaunarta.

Post a Comment

Previous Post Next Post