Naushi Fassarar sultan Indian Hausa Sauke Anan

   NAUSHI (Sultan) Yau Yakama ranar labara ,ikram ta shirya gagarumar walima ma Amarya da ango, a babban masallacin nan na sultan bello ,k'arfe 4 na yamma ,abokanan ango suka fara jigila na d'aukan k'awayen Amarya da 'yan uwanta zuwa wajen walima ,ciki hadda Mr judge ,shine ma babban abokin ango ,sosai walimar tayi armashi ,Amarya da k'awayenta sunsha kyau gwanin ban sha'awa ,shkeikh Kabir haruna gombe tareda alaramma Ahmed sulaiman ne suka gudanar da wa'azi me shiga jiki akan aure, alhamdulillahi anci ansha walimar ,taro yayi taro an watse lpia.

  Ba a sake wani event ba se ranar jummu'a ,tinda safe akaje gidan su ikram wajen k'unshi ,inda shima sun tarar Hajiya tasa antarbe su da abubuwan motsa baki ,kama daga su donough, cup cake, sinasir, samosa etc, da kayan drinks ,daganan gidan su ikram suka shirya tsaf Dan wucewa wajen kamu ,Wanda aka shirya a msquare...

 Ranar asabar akayi me kankat yaune ranar da aka dauran auren *Khadeeja da sulaiman da jawad yasir*,alhmdl taro yayi taro anci ansha biki yayi armashi ,da daddare aka dauki Amarya zuwa gidan mijinta ,nanfa muka ga kukan rabuwa tsakanin ikram da Khadee seda k'yar aka rabasu ...

 Washe gari ikram suka shirya zuwa gidan Amarya Khadee ,basu suka baro gidan ba seda yamma ,seda suka tabbata sun kammala mata dik wani aiki kafin suka mata sallama suka kama hanya ,itadai ikram daga nan kai tsaye gidan su ta wuce ,Dan acewarta ai anriga angama komai ,tanaso tad'an hutu ,saboda tinda aka fara bikin Khadee atsaye take ,wannan ne yasa tayi sallama dasu mamansu Khadee ,sunyi godiya sosai kafin aka ba ikram kayan bikin Hajiya ta kaimata.

  Ikram matashiyar budurwa ce me k'arancin shekaru ,amma me hankalin manya, macece me son addini da sanin yakamata ,a yanayinta kuma ita ba fara ba can sosai ba kuma za'a kirata da bak'a ba ,sedai mu kirata da wankan tarwad'a ,ba tada wani tsawon azo agani ,sannan tanada k'aramin jiki ,zuciyarta me kyau ce kamar yadda komai na jikinta me kyau ne da d'aukan hankali ,bata cika son haya niya ba ,amma kuma akwaita da son hira ,tanada son barkwanci kuma. Kad'an kenan dangane da ikram!!!


 Bayan shekara biyu
 
Su ikram sun kammala makaranta ,a yanzu haka tana matsayin dentist ne wato likitan hak'ori, a inda take aiki awani asibiti na k'awar Hajiya wato *AL-MUNIFF* hospital.

  Hajiya ce zaune a parlour tana tinanin wani al'amari daya d'aure mata kai ,na cewa ,yau ikram nada shekara ishirin hadda biyu amma har yanzu ba wani zancen aure, abun na damunta kuma ta kasawa xama tayi maganar da ikram ,ba tin yau ba tin kwanaki ,taji ana ta cecekucen wai dik Wanda yazo neman ikram wani mak'wacin su ne ke zagayawa yana b'atawa ikram suna ,da cewar wai ita 'Yar macece ,ba tada uba ,ranar da Hajiya Ameena taji labarin ,ba k'aramin tashin hankali da damuwa ta tsinci kanta aciki ba ,wani lokaci wasu magulmatan da basa iya hak'uri su kanzo wada Hajiya da maganar wai halan mahaifin ikram rasuwa yayi tace

Post a Comment

Previous Post Next Post