RagarGaza Fassarar Sultan Indiyan Hausa film 2022

   RAGARGAZA 1&2 (Sultan)

Duk Wanda Yakeso wannan Fassarar yaje Yakalli Videonmu na YouTube, Karku manta Zaku iya Kallo Dakuma Saukewa Acikin wayanku dakuma Komfuta Cikin Sauki Sabuwar Fassarar Sultan Fassarar Kamar Yadda Akasaba AYau Muna dauke muku da Kayataccen Sabuwar Fassara Daga Kanfanin Sultan film factory, Jama'a Barkanmu da Shagalin Karamar Sallah, Ubangiji Allah Yamaimaita ma, Mu dage da Yawaita Aikin Alhairi da Neman Lada Akodayaushe.


Sai Anan ne zaku More
Malam muhammadu Dan asalin jigawa ne yanada mata hudu da tarin yara matarsa ta fari nada yara shidda maza ta biyu kuwa yaranta tara bakawai mata biyu maza ta ukun nada yara biyu duk maza sai Amaryarsa dake da yara goma sha daya tara maxa biyu mata Alhmdlh gidan akwai zaman lfy da hadin kai domin ya gina gidansa da zaman lfy dazumunci mariya itace matarsa ta uku itace keda yara biyu inusa da Auwalu duk cikin matan sa tafi hakuri da kawaici hakan yasa yaranta suma sukayi sanyun hali irin nata sam basu da hayanikuma dukansu manoma ne sosai yayin da dukansu sukai aure kuma barakallah dukansu suna nan da rai malam inusa nada mata daya wato saude Allah be azurtasu da haihuwa ba tsawon lokaci sai daga baya suka fara samu amma kuma yaran wabi sukeyi saida tayi haihuwa hudu haka kafin daga baya tasamu cikin dijee cikin hukuncin Allah kuma ita ta rayu khadija ta taso yarinya kyakkyawa fara ce sol irin fararen nan ne sosai sai dai fa batajin magana duk wata tsokana da caskale ta kware akai dan haka yara sa'anninta ke tsoronta inda har suka samata suna bata sani ba wato uwar mazga.

   Acikin 'ya'yan malam muh'd dayawa daga cikinsu sun sami cigaban rayuwa inda sukayi karatun boko wasu sun sami aiki a birni wasu kuwa kasuwanci yakaisu kuma cikin ikon Allah ansami daukaka da wadata inda malam muhammadu yake da matansa suke samun kulawa a yanzu haka shine matsayin me gari wanda su habeeb 'ya'ya ne ga dansa babba wato khamis dake aiki a abuja sam basu dade da dawowa daga U.S ba inda suka shafe shekara goma sha biyu a can dan a can sukayi karatun su na secondry har zuwa jami'a indadukan su suka karanci fannin likiktanci shi habeeh ganygoicial shi kuma Naseer consultant ne yanzu haka satinsu biyu da dawowa shine suketa zaga dangi dan suna son kauye basu da kyama sam.

cigaban labari

   Uwar mazga nata sharar bacci cikin baccin ma mafarkin su habeeb tayita yi wai har da zawo naseer yayi aikuwa take ta qara rushewa da dariya wadda ta qara jawo hankalin inna ganin da tayi tanata bacci ba ruwanta yasata tashinta dan itafa ta gama gasgata aljanu ne da dije.

   Inna saudi ce ta fito dauke da kwarya cike da fura inda dije dake zaune gefen babanta yana cin tuwo tanata zuba mishi surutu inna saudi tace malam na fito bari inyi sauri inje in dawo inga jikin nasu dije taso muje ki rakani dan dare ne yanzu yafi mu tafi mu Biyu, ah ah ni ba inda zani ai munyi fada da baba malam shiyasa jiya da hafsi tace min dijangala tame gari na barar mata da gari ni yanzu nayi yaji saiya zo biko 


dariya sukayi dukansu inda malam inusa yace yi tafiyarki kinji kyale wannan uwar rigimar ai bama saika ce ba ni nayi gaba saina dawo a dawo lfy innata Allah yasa tasa kai ta fice, gyara zamanta tayi tace baba wai ni waye beda lfy ne a gidan me gari ?

yayyenki ne na abuja wai gamo sukayi da aljana a hanyar su ta shigowa gar......ai be qarasa ba yaga ta mike ta suri takalma tana bari inje in raka inna sai na dawo ta zura da gudu tabarsshi da sakin baki kafin daga baya yayi murmushi yace Allah ya shiryamin ke dije ta.

  Bata riski inna a hanya ba dan ba hanyar datayi tsammani tabi ba kusan a tare suka isa amma innah sam bata ganta ba ta shige gidan bayan sun gaisa da surikanta ta shiga bangaren mai gari ta gaisheshi tare da su habeeb wadanda suka warware amma kumburin bakin habeeb na nan idan nasir ya kalle shi saiya qara fashewa da dariya iya kuluwa habeeb ya kulu jiyakeyi inda ba aljana bace tayi musu haka ba wlh da mutum ne bema san me zaiyi masa ba a haka inna ta musu sallama tana dada jajanta abin kafin ta miqe tayi musu sallama ta fita 

  Akofar gida ta riski me gari zaune bisa kujerar sa ta tsoffi ta lababa ta shige gidan indayana kallonta amma ya qyaleta dan yasan halin mutuniyar tunda bataso kulashi ba toh gara ya kyaleta 


Post a Comment

Previous Post Next Post