Rukunin Dambe Fassarar Indian Hausa 2022

   RUKUNIN DAMBE (Sultan)


Kunji wannan kuwa?
Kamarsu ce Daya
  Hanyar Abuja Can cikin daji akwai wata ruga ta yan Fulani usul ciki,amma duk da haka rugar a kusa da gefen titi take,tana da girma ba laifi,harda makaranta primary da secondary tare da islamiyya,Fulanin dake wannan dajin ko hausa kadan suke ji basu iya sosai ba amma suna Jin hausar,
  
  Wata Dattijuwa ce kyakyawa me cikar haiba ta fito domin zuwa asibiti dake Suleja Hanyar Abuja kusa dasu,Dattijo yana rike da hannunta da Alama mijinta ne sai sannu yake mata,haka suka shiga mota har suka karasa wannan asibiti,bayan an duba Lafiyarta an tabbatar rashin haihuwa ce ta kawota tunda likita yace baza ta taba haihuwa ba haka ma mijinta shima,cike da tawakali suka siyi magunguna suka fito wajen me gadin wannan asibiti suna hira dashi sama sama,me gadi ya kalleta tare da cewa Hajiya idan baza Ku damu ba ko zaki iya rike min yata guda daya danake da ita?tunda bakya haihuwa kuma na yaba da halayenku zan baku tarihina idan kun amince sai na bar muku yata kyauta Ku riketa Amana.
    Sunana Ahmad wanda akewa lakani da Tall Man a cikin Garin Borno muke da dangina tare da dangin matata wacce Allah yayiwa rasuwa kwanan nan,Matata yar Asalin Nijar ce buzuwace gaba da baya amma danginta kaf suna Borno a unguwarmu,Yan uwanta da kuma kanin babanta sai sauran danginta amma iyayenta dama sun Dade da rasuwa,Bayan munyi aure da shekara biyu Allah ya bata ciki ta haifa min yata sunanta Salma watan Salma 7 a duniya Allah ya karbi rayuwar matata Khairat wacce Hawan jini ya kama da karfin gaske,
   
 Bani da Uwa bare uba nima bani da yan Uwa mata sai maza a zamanin nan idan na bawa dan Uwana namiji rikonta matar zata iya gallaza mata tunda ba shine zai zauna da ita ba,haka idan nayi aure ban san wa zan aura ba,haka na hakura na bawa dangin matata Khairat yata Salma,amma yau Salma shekarta biyu a duniya wahalar rayuwa take Sha a hannunsu rayuwar yanzu ba imani ba tausayi

  Idan kun yarda muje garinmu kuga gidanmu ayi yarjeniya da dangina da dangin matata kusan juna sai ku tafi da Salma wajenku Ku rike ta Amana,sai Ku dinga kaita wajen dangin ubanta dana uwarta suma zumunci kawai amma na baku ita halak malak Allah yayi jagora kune iyayenta daga yau,Murna wajen wannan dattijai ba a magana,kamar wasa ya dauki Hutu washe gari suka tafi har Borno state,Dukka sun gaisa da danginsa dana Khairat Babar.
  
 Salman, hannu biyu suka karbesu amma da gani Salma a cikin wahala take ba a kula da ita Sam,haka yayi musu bayani ya dauki Salma da kayanta na sawa ya bawa wannan dattijai da sharadin zasu dinga kawo Salma ana gaisawa da danginta suna zumunci,cikin dangi babu wanda yace kar ayi haka su zasu rike kowa mukus yayi harda fatan alkhairi,cike da murna dattijai suka koma gida suka nuna Ahmad Tall Man baban Salma ga kowa dake da alaka dasu a rugar Fulani duk da cewar yan uwan nasu suma kusan duk sun kare sai kadan daga ciki sai makwafta da abokan arziki.
     
    Kamar wasa tsakani da Allah suke rike Salma ko yarsu baza taji dadi haka ba sabo da gatan da suke nuna mata,ubanta Tall Man idan yazo ganin yarsa dadi yake ji ba kadan ba yana shi musu albarka,haka mutanen gari ma,Salma sai abinda take so shi yasa ta taso cikin shagwaba da tabara ta gaske,amma suna bata tarbiya ta gasken gaske, tana da shekara biyar suka sata a schl tana ilmin addini dana zamani,kamar yanda alkawari yace suna kai Salma Hutu cikin danginta tayi Hutu acan,duk Hutu a Borno take yinsa Affa da kansa yake kaita can abin sha'awa.

   Tana da shekara takwas Ahmad Tall Man mahaifin Salma ya rasu sakamakon ciwon Koda daya kamashi ba tare da doguwar jinya ba,masu rikon Salma sunyi kuka sunyi zaman makoki,Salma tana primary 4 aka fara ganewa kamar tana da tabin kwakwalwa,sai aganta tana ta maganganu ita kadai,ko aga tana dariya ita daya, wani lokacin kuma tayi ta kuka tana shagwaba,sai ta dinga kallon waje daya, watarana kuma tayi ta wasa tana maganganu kamar da wani takeyin maganar,sai aga tana shafa iska ko ta rungumi iska, a school ma haka takeyi,watarana kuma aji tana ta rawa tana cashewa kamar tana Jin kida har karkata kunne takeyi,bata da kokari a sauran Subject da dama banda English da French,amma fa Idan anzo exam,a class duk tambaya zata amsa amma kuma bata da kokari kan kowanne subject sai dai English kadai sai French idan ana musu,har kure malamai takeyi indai akan yare ne to baka isa ka kureta ba.
    
    Haukar Salma bata kara ta'azzara ba sai da ta shiga js1 nan aka fara kiranta da living things,sabo da bata iya ba,ance what is living things? Salma tayi sauri ta mike cikin iyayinta tace Living things cike da shagwaba, tace living things is a living things that live on earth with a life, akwai aka kwashe da dariya sabo da Salma kowa yasan a exam kadai take kokari ta cinye du ana mamakin hakan,
   
 Gata dakikiya a class amma da anzo sauran Subject sai ta koma jaka sentence daya baza ta iya kawowa ba bare ta bada definition na abu, sai languages, wani lokacin ma gani za ayi ta tsurawa waje daya Ido tana murmushi ko tana Surutu kasa kasa, kayi mata dariya taci ubanka tana da karfi idan tsokanarta kayi amma idan ita ta tsokaneka to sai ka mata duka baza ta iya komai ba,wasu har suna cewa Aljanune da Salma living things, Sunyi wani Sabon Malami komai sai yace collaborate, shine kullum Salma ta rike aikinta tace Collaboration,shike nan wannan sunan ma yabi Salma,Salma Collaborate ko Salma Living things.

     Salma tana da hakuri da Hankali, bata Harka da kowa daga iyayenta da suke riketa shike nan kowa nata ne ba ruwanta da duniya da abinda ke cikinta ,Salma me tsananin kyau ce na gasken gaske, fara ce ba fara can ba normal farinta yake,hanci me kyau dan dai dai dashi,bakinta dan karami me dauke da kananan hakora masu kyau farare,tana da Dimple, Skin dinta luwai luwai ,doguwa da ita ba siririya ba ba ramammiya ba, gashinta ya wuce kafada baki me kyau da santsi,ga wani kwantacce yalala a gaban goshinta dankwali baya iya rufewa har wajensa, idan kaga Salma sai kace yar kasar Ethiopia ce skin dinta da ko irin nasu ta hadu karshe a Ethiopia ma sai kyakyawar gaske za a samu irin Salma komai yaji ga uban Hips.

    Salma bata da makusa sai dai akwai babbar matsala Salma bata Sallah ko kadan,duk yanda ka damu da tayi Sallah to baza ta taba yi ba,haka duk wani abu da ya shafi addini bata yi,yin duniya baza tayi ba,ko na ganin Ido sai taga dama,tana da surutun tsiya idan ta samu waje fadi ba a tambayeka bace,komai ta fada idan taga dama bata da sirri,haka ga tambaya har tafi dan jarida amma ba a gane hakan sai Salma ta aminta da mutum sosai zatayi ta zuba har sai ya gaji. Halayen Salma kenan zaku iya tsintar wasu a cikin novel nan gaba.

Post a Comment

Previous Post Next Post