Safara Sabuwar fassarar Sultan Indiyan Hausa 2022

   SAFARA 1&2 (Sultan)

Alhini

  FCT Abuja unguwar sai wane da wane a Abuja ma sai ka Isa kake zama cikinta ba kowanne me karamin kudi ke iya zama ciki ba sai ka sharaha ka gawurta kuma ka tumbatsa ka fetsara a Naira zaka iya zama cikinta,ba wanda zai zaton cewar a kasar nan akwai unguwa me tsari da kyau irin nan ba ko a turai sai haka,shi yasa ma kafin kaga bakar fata a unguwar zaka dade kusan duka fararen fata ke zama a wannan unguwa irin su Ambasadors,consilor na embassy da Sauran masu zama a kasar Nigeria lokaci zuwa lokaci,wani tsantsararren gida da kusan ma yafi da yawa kyau a layin,wasu motoci ne sunfi biyar tafka tafka suka shararo zasu shiga wannan gida wawakeken gaske tsayawa fada muku tsaruwar wannan gidan kadai zai cinye mana Pages duka ma, remote.

  Driver me jan motar gaban ya danna sai ga gate ya dage sama,suka shiga wannan gidan wanda ko ina motocine na alfarma,gidane na nunuwa a duniya,tunda motocin suka shiga ko ina ma'aikata da Securities sun dai daita sahunsu suna jira me gidan nasu ya fito,sai da aka dauki kusan 30mnt bai fito ba har an kosa da jira su kam da Alama sun saba da hakan.

   Kofa aka bude masa ko ina ka juya Sojoji ne a gidan ana tsaro,kafa daya ya zuro hakan ma ya dade bai fito ba sai daga bisani ya zuro kafar dayan ya fito a gadarance cikin Isa da takama yana shan kamshi yana basarwa,wow Tabbas wannan Bature ne ko balarabe babu abinda ya hadashi da suffar bahausa ko jinin Nigeria,domin ta ko ina ba kalar nan bane,cikin turawa da Larabawa ma sai an dage da gasken gaske za a samu me kyan wannan matashi,domin wasu ma da dama zasu ce Aljani ne,za a iya karade kasar nan kowa zai iya cewa Bai taba ganin me kyau irinsa ba,kamar Aljani haka yake,tun daga dirinsa da baiwar sura cikar zati da haiba baza ka gama rudewa ba sai ka kalli fuskarsa,dole kayi kabbara ga Allah,iya saninka wannan.

    Matashin ya zarta saninka a baiwar kyau idan ya shugo waje ko waye sai ya raina kansa Bai isa ya matsa kusa dashi ba, hancinsa codede zarkadede,dan bakinsa cut dashi pink kamar yasa jambaki,idanunsa Dara Dara shanyayyu kamar bacci zai yi,sumarsa me uban yawa baka me santsi tasha gyara Naira tayi kuka a kanta,ga wani hadaddun Saje da gemu nasa, kafafunsa da yatsunsa abin kallo,girarsa kuwa har hadewa take sabo da baki da yawa,gashi fari kar kar dashi ba irin fari na jigari jigari ba farin bature ne dashi domin yafi Balarabe fari,amma kyansa da cikar hallitar kamar Balarabe,ba zai wuce 32years ba.

  Gaisuwa ake kwasa cikin harshen turanci amma ko saurarensu baiyi ba fuska ba rahma ya shiga cikin palon tare da danna code din kofar cike da takama da gadara, sai ka shiga palon zaka San ma a duniya kake ne wai ko a Aljanna domin kyansa da tsaruwarsa ya wuce hankali,kamshi ne da sanyi ke tashi kawai,

    Wata budurwa ce kyakyawar gaske ke zaune a palon ta nitse cikin kujeru kafa daya kan daya tana cin Apple tana kuma danna kafcececiyar wayarta,tana ganinsa ta Mike tare da Fadawa jikinsa cikin harshen turanci take masa sannu da zuwa,dan murmushi yayi kadan,cikin hausar daya fara koya Bai iya ba yace yau...Shi..ni...kinka Jo?wai yaushe kika zo yake nufi,Budurwar tace since in the morning,ci..danna...mini... English,(ki daina min English). Kansa ya nuna da yatsa ni...sho nace na gane..hausa, dariya tayi ita dai hausar sabon saurayinta na bata dariya,ba haka ake cewa ba Honey,cewa zakayi ina so na iya hausa ki daina yi min turanci.Ok na gano shi(na gane) na gane zaka ce.

   Wuyansa ta sakalo cikin salo ta fara aika masa da kiss ya fara biye mata kenan yaji kamar an rike masa harshe tam,da kyar ya finciketa daga jikinsa yana huci kamar zaki,bata gane ba Sam ta kara rungumeshi nan take taji anyi jifa da ita gefe can har sai da kanta ya bugu da bango,ihu ta saki tare da rike keyarta ta dago tana kare masa kallo,honey lfy kake kuwa?jiya fa muka hadu ka bani address kace nazo mu dan huta muna mu'amula daga nan ma sai ka koyi hausa duk cikin turanci take kora masa bayani,cike wulakanci da isa,izza da gadara cikin lalacacciyar Hausarsa wacce a dole sai ya koya yace ni...ni...ba Jan iska bane,ta tari numfashinsa to kai ba dan iska bane ni kuma itace?, cike da takaici yace ni bana cinye mata,nan take ta kwashe da dariya sabo da hausar abin dariya,shi kanshi sai da yayi murmushi,wai haka hausawa suke cewa.

  Tace to ai ba haka zaka ce ba na gane baka sex amma zamu iya Romancing ko? Baki ya tabe tare da cewa nop. ni bana con ina tabo mashe ne, cin can me na Shana? tace a'a Banason nono irin naki, tunani ya fara na Kalmar da zai ce yace ayi maka surgery noanoa naka naki yana kamar da tsayi har cikinka ni na fada ma fact that komi ma Bana con shi na taba masha, ina feeling Bana so temper na yana rising,what do u people called it?I wanna know?

  Harara Ruky baby ta watsa masa sabo da ta gano tsab ci mata mutunci yakeyi baya son ta dan dai ba Jin hausa sosai yake ba,wai ayi mata plastic surgery a breast yake nufi nata ya zube,kuma baya son komai ba dan iska bane shi,tsaki taja tare da mikewa ta fice fuuuuuuu tare da shiga motarta ta bar gidan,tana cewa ita dashi har Abada dama haduwarsu ta farko kenan a resturant,dan iska har ita zai ciwa mutunci amma tana mamakin karfinsa yanda ya jefar da ita kamar Aljani daga tabashi taji wata iska ta fisgeta ta makata a bango,kai gaskiya Aljanune da shi,taya kamar ta zai ce mata boobs nata har ciki,ita da bata da girman su ma har magani take Sha dan su kara girma sai dai idan idonsa ne ya nuna masa haka,Ruky sai masifa take tana driving dama kallonsa tayi kalar kyau da gani gwarzon namijine gashi me kyau,ga kudi idan suka saba gaskiya ta more yanda zai dinga biya mata bukatunta na masha'a kuma zai tafi da ita kasar su ma suci gaba da Jin dadinsu ga Naira wannan ya cuceta dakikin banza a haka kamar gwarzo Ashe lagwani ne.

  Shi kuwa wannan Matashi tana barin gidan wani farin ciki ya ratsashi kamar an masa bushara da Aljanna, bedroom ya wuce wanka ya fesa sama sama ya shirya kansa Ashe musulmi ne sai gashi yana sallah sosai karatun Qur'anin sa abin saurarone sabo da dadin muryarsa ba a cewa komai sai masha'allah,yana idarwa ya fara azkhar ya dade sannan ya gama ya fada saman bed tare da jawo wayarsa ya latsa number lovely M,hello Sweet heart cike da shagwaba kamar zai yi kuka ya fara magana kamar wata mace haka yake shagwaba har yafi matan ma,Sweet heart am tired of this country gaskiya,My Son na fada ma ka daina min turanci Hausa zaka yi min so nake ka iya min yaren hausa, ur mother's tongue shi yasa nace ka fara aiki acan sabo da so nake ka iya yarena kuma ina so ka saba da kasar sabo da soon zamu dawo kasar Nigeria gaba daya da zama tunda.

  Abbanka ya rasu me zamu zauna muyi,idan kana son yan uwanka kazo ka kawo musu ziyara,amma bazan zauna a kasar nan ba Nigeria zan dawo gwara ma ka saba,ya aikin? Alhmdllh sweetheart da wa'ala aiki,not wa'ala wahala,tun kana karami NA'IM nake koya ma Hausa amma ka kasa koya amma bari zamu dawo Nigeria ne zaka iya dole.,My love pls ba dadi kasar nan me zamu dawo muyi?tunda ina da kudi kema kina da shi me zamuyi kuma pls Sweetheart idan kina so na zauna ki dawo kasar to I missed u, miss ur food badly Dear.

      Oh! My son ka jirani zan dawo duk abubuwanka zan taho dasu ba sai ka dawo ba, kai kam ka dawo Nigeria kenan,ka jirani nan da 3wks zaka ganni Insha'allah,Kukan shagwaba ya fara mata shi sai dai yazo ya taho da ita,kashe wayar tayi cike da farin ciki.

Post a Comment

Previous Post Next Post