Sassauci Sabuwar Fassarar Indian Hausa 2022 Indiyan Hausa

   SASSAUCI 1&2 (Sultan)Abun Mamaki Gantalalliya

   Wata zukek'iyar bakar mota kirar benz E350 na hango ta karyo kwana, wani dankareren gida ta tsaya, yana matsa horn mai gadi yataho da gudu ya bude gate, sannu da zuwa yakeyimas bai tsaya ya sauraresa ba ya wuce inda ake parking motoci. Maigadin yana rufe kofar yabi bayan motar da sauri, kan ya isa har mutumin dake cikin motar ya fito, gaishesa yayi tare da yimasa sannu da zuwa. "Yawwa sannu sabo, madam tana ciki ne ko tafita" yake tambayar mai gadin, daidai lokacin dayake bude kofar bayan motar yana dauko jakar sa.

"Ai ranka shi dade baka dade da fita ba wata mata tazo naga sun fita tare, kuma har yanzu basu dawo......." daga mishi hannu yayi rai abace yace "shikenan nagode zaka iya tafiya" Yana shiga cikin gidan, tundaga bakin kofa yafara karo da shirgi kalakala, tsaki yayi ya wuce dakinsa, wanda yasameshi a yanda ya fita ya barshi, wani takaici ne ya rufeshi, kamar yayi kuka, ga yunwa daya kwaso.

Da kansa ya kyara dakin sannan ya fito kitchen domin yasamu abinda zaisa a bakinsa. Yana shiga idonsa ya kai kan gas cooker din, tayi dak'al dak'al, dagani tunda aka siyeta bata taba ganin ruwa ba, haka ya daure ya dauko wata yar karamar tukunya, itama seda yadaurayeta sannan ya dora ruwa, wanda baima san abinda zae dafa ba.

    Fridge din ajiye kayan miya ya bude don yaga ko zae samu ragowar miya sai ya dafa farar shinkafa, yana budewa ya rufe da sauri, dan tsabar wani wari daya doshi hancinsa, nan take yaji amai ya taho mai, da gudu ya kashe wutar gas din yayi waje da sauri.

    Tun a kofar kitchen din yafara sakin aman, ga wani jiri dayake dibarshi, haka yayi yagama, da kyar ya gyara wajen yayi dakinsa, toilet ya fada ya sakarwa kansa shower, sannan yasamu ya dan ji dadi. Yana fitowa ya suri key din mota yayi waje, ba motar daya dawo da ita ya hauba yanzu, wata jar mota ya dauko an lullubeta da bakin tinted, yana fita bai tsaya a ko ina ba sai a chicken castle.

     Anan yasamu yaci sakwara da miyar agushi, ci yake kawai amma zuciyarsa babu dadi. Yana gamawa ya koma gida, misalin karfe 6 na yamma, amma bata dawo gidan ba, sai yayi tunanin ya kirata a waya sai kuma ya fasa. Kwance yake akan gadonsa kamar mai bacci, amma kuma ba baccin yakeyiba illa tunane tunane da suka shige mishi kai. Ba ita tadawo gidan ba sai goma saura yan muntina.

    Buzubuzu ta shigo gidan, daganin tafiyarta kasan babu nutsuwa atare da ita, gashi sai taunar chew gum take kai kace ba mace ba, bama wannan ba, shigar da tayi ma kadai ya isa kasan wacece BINTU MATAR SADIQ.

Dakinta ta wuce tayi wurgi da jakar hannunta tana "washhh!!! Nagaji wallahi" kayan jikinta ta cire ta wurgarsu a tsakiyar dakin,ta dauko wata doguwar rigar bacci,wacce inbanda tsami babu abinda takeyi, amma haka ta tafka abinta ko ajikinta. Kan hargitsetsen gadonta ta hau ta kwanta abinta, wayarta ta dauko takira wata kawarta, saidai bata dauka ba, haka ta gaji ta ajiye ta ja bargo ta shige.
Shikuma tunda yaji shigowarta yakasa daurewa seda ya tashi ya biyota har dakin nata. A fusace ya shiga kamar wanda zai daketa sai dai yana zuwa yaji gabansa yayi wani irin mugun faduwa,a sanyaye ya karasa gabanta.
   Haba bintu! Ina kika tafi kika kai dare haka batare da kin sanar dani ba" shiru tayi kamar ba da ita yake ba, seda yasake magana ta dago a fusace "haba malam kafa takura min nidai wallahi, nadawo ma ko sannu da zuwa baka min ba sai tambayar daga ina nake, to unguwa naje koda magana ne? Girgiza mata kai kawai yayi kafin yace "Allah ya baki hakuri" tsaki taja "aikin banza kawai, nikatashi kafitar min adaki bacci nakeji" bata jira cewarsa ba taja bargon ta koma.

Salalo salalo yatashi yafita adakin, dakinsa yakoma ya kwanta yana tunanin, wai maiyasa bintu take mishi kwarjini ne? Meyasa idan yayi yunkurin yimata fada yake kasawa ne? Meyasa kuma yake masifar sonta? Da wannan tunanin har bacci ya kwashesa amma bai samu amsar tambayarsa ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post