Abun Mamaki Sarauniyar Kyau 2022 Ta Dole 37 Yan Takaran Kyau: Ade Eme

 DA DUMI-DUMI: Ada Eme ta zama Sarauniyar Kyau ta Nijeriya a Shekarar 2022.

Ada Eme, wadda ta fito daga jihar Abia ta lashe kambun The Most Beautiful Girl in Nigeria (MBGN 2022) a jihar Legas ranar Juma'a, kamfanin Silverbird ke shirya gasar duk shekara.

Ada Agwu Eme ta zama mafi kyawun yarinya a Najeriya, MBGN, na 2022.

Ada Eme, wanda ya wakilci Miss Abia, ta doke sauran ’yan takara 37 da suka fito daga sassan Najeriya domin neman kambu a daren Juma’a, a Otal din Eko da Suites da ke Legas.

Ada ce za ta wakilci Najeriya a gasar Miss World mai zuwa, yayin da Montana Felix za ta zama wakiliyar Najeriya a Miss Universe.

DAGA Saliadeen Sicey

Post a Comment

Previous Post Next Post