Fafatawa Sabuwar Fassarar Sultan Indiyan Hausa

 Fafatawa Fassarar Sultan

  Kamar yadda muka sani kuma muka saba, wannan bawan Allah Wanda mukafi sani da suna baya goya marayu akoda yaushe yana iya kokarinsa wurin ganin ya kyautatawa rayuwar marayu sannan kuma ya sadaukar da dukiyarsa wurin taimakon musulunci, kamar yadda nadade ina fada muku shi wannan bawan Allah matashine ba tsoho ba kawai dai Allah ne ya albarkaceshi da halin manya dan haka muyita yimasa addu'a akan Allah ya albarkaci rayuwarsa da dukiyarsa da kuma iyayensa. Amin.

Dukkan jama'ar dake wurin suka amsa cikin farin ciki domin wannan bawan Allah ba karamin taimako yake yiba saboda kusan agarin ma shine lamba daya wurin taimakawa rayuwar marayu.


Saida aka gama rabawa marayun kayayyakin da aka kawo musu akan idon wakilin wannan bawan Allahn dake basu gudun mawa wanda suka dade da rada masa suna da baya goya marayu, bayan gama rabon kayan tsaf sannan wakilin baya goya marayu yatafi, sukuma yaran kowa ya kinkimi kayanshi ya nufi wurinda zai adana su, haka suke gudanar da rayuwarsu cikin wannan gida wanda a lokuta mafiya yawa sukan shafe sama da watanni biyu batare da sun samu wani tallafi ba indai ba wannan bawan Allahn ne ya aiko musu ba gashi kuma duk wannan hidimar da yake yi musu basu taba ganinsa ba balle har su gane kamannin.

  Kamar bazai taka k'asa ba haka yake tafiya, sanye yake cikin jar t shirt mai dogon hannu yasha d'amara da jar belt wadda ke d'amare ajikin bakin trouser din dake jikinsa, duk da wai ahakan sauri yake amma baisashi sauya salon tafiyar tashi ba,bak'in face din dake idonshi yadan gyara bayan ya maida hankalinsa kan agogon azurfar dake d'aure a tsintsiyar hannunshi, kamar koda yaushe fuskarshi babu alamun fara'a atare da ita.

Kofar da zata sadashi da falon mahaifiyarshi ya bude ya shiga fuskar nan kamar zaice wayyo Allah dan tsananin fushi

Ganin babu kowa aciki yasashi kara yin gaba, awani tsararren falo wanda aka tanada musamman domin hutawa ya isketa, tana zaune saman kujera daga ganinta bazata haura shekaru 45 ba aduniya, farace jajur mai dan jiki, tana sanye da wani leshi mai tsadar gaske, wuyanta da hannuwanta gamida kunnenta duk gwala gwalai ne sai walwali suke, haka yan yatsun hannunta ma duk sunsha zubunan gold,gefenta kuma wata yar matashiyar budurwa ce wacce zata kai shekaru 23 tana kwance tayi matashi da cinyar matar.

  Sallama yayi wadda ba lallai su iya jiba domin aciki ciki yayita Dukkansuhankalinsu yana ga drama din da suke kallo atashar tauraron dan adam wanda har saida ya zauna sannan suka farga dashi...

Post a Comment

Previous Post Next Post