Garnakaki Sabuwar Fassarar Sultan

 Cikakken Labarin

Da alama ranta a b'ace yake ga k'aguwa a zahirinta ya bayyana, sake kallon agogo tayi na karo ba adadi sannan ta kalli k'ofar douche d'in taja dogon tsaki tana magana k'asa k'asa "wannan wulak'anci dame yayi kama, sama da awa d'aya kina wanka, ki bani wani banzan serviette (towel) na rik'e kamar ke wata musaka ce.

 Sake kallon agogon tayi sai dai kafin ta maido kallonta taji an bud'e k'ofar douche ana fitowa, da sauri ta kalleta amma saboda ganin santaleliyar budurwar ta fito daga ita sai d'an k'aramin silip (pant) d'inta ko soutien ( bras) babu yasa tayi k"asa da kanta, ita kam ko a jikinta takowa tayi ta zo gabanta ta karb'i serviette d'in ta d'aura a k'irji sannan ta karb'i dayan ta d'aura a kanta, gaban coiffeuse taja kujera ta zauna tana kallon madubi ita kuma mai aikin ta matso ta d'auki mai ta fara shafa mata, bayan ta gama ta shafa mata powder da pink d'in jan baki, ta fito mata da wani silp d'in da soutien ta bata ta saka sannan ta fito mata da riga da siket na atamfa.

  Dinki ne na yan zamani yayi kyau sosai gashi ya zauna a jikinta daram , mai aikince ta zuge mata zip d'in dake bayan siket d'in wanda ya kamata sosai komai nata ya fito masha Allah, d'an kwali ta kashe d'aurinshi sannan ta fito mata da sarka da yan kunnai da gani kasan sunji kud'i, sannan ta fito mata da jaka da takalmin da suka dace ta aje mata gabanta, sakawa tayi sannan ta d'auki turare ta fesheta dashi ita kam tana tsaye kamar gunki, tana kamalawa ko jiranta bata tsaya ba kawai tayi k'ofar fita abinta.

Binta tayi da harara tana fad'in "wannan zanso naga gidan aurenki , mijinki ne zai miki wannan hidimar ko kuma mai aiki zai samar maki."


Gyara d'akin tayi kamar yanda maishi zata buk'aci ganinshi sannan ta fito ta rufe mata d'akin. 

Ba tare data kalli kowa dake kan table a manger (dinning) d'in ba taja kujera ta zauna, wata mai aikince dake tsaye kusansu ta matso ta fara zuba mata abincin, ta zuba mata fritte zata bud'a wani kwanon kawai ta d'aga mata hannu tare da kallonta cike da wulak'anci tace, Ya isa haka, ni ba jaka bace kamarku da zan zauna ina had'iyar abinci haka.

  Ja baya tayi kanta k'asa bata kalleta ba ita kuma ta fara cin fritte d'in, mahaifiyarta ce tace "mu kike so mu fara gaidaki kenan? Cike da nuna an takura mata tace ina kwana. Mamar ce tace nice kad'ai a wajen?

Kallon saurayin da suke fuskantar juna tayi, amma ganin wani kallo da yake mata tare da murmushi yasa ta zabga masa harara, maida kallonta tayi ga mahaifinta, d'auke kai tayi ta kalli mahaifiyar tata tace "ki tabbatar min jiya bai shigo cikin maye ba, ni kuma saina gaisheshi."

A tsawace uwar tace "ke, ashe baki da mutunci, wannan ba mahaifinki bane da zaki fad'a masa haka?" A wulak'ance ta kalli uwar tace "shi kenan mutunci ne yake sashi shigowa cikin gida a buge? kinga nifa karki b'ata min rai da safiyar nan."

Duk da k'ok'arin rik'e hawayen da tayi saida suka zubo, cikin muryar kuka tace "ba laifinki bane, kiyi yanda kike so."

Tana fad'a ta juya ta nufi d'akinta tana zubar da hawayen takaici, ita kuma ko kulata ba tayi ba bare taji ba dad'i, saima mahaifinta data kalla tace "zaifi maki kyau ki daina saka damuwa a ranki akan wannan da baisan kina yi ba." Tashi tayi ta bar abincin zata fita ,mahaifinta ne kalleta a marairaice yace "kiyi hak'uri mana gimbiyata, nayi alk'awari ba zan sake ba."

Kallonshi tayi ta kalli saurayin dake zaune kusanshi tace "ka fad'awa wannan wawan watak'ila shi zai yarda da abinda ka fad'a, amma bani ba *Khairat*. Fita tayi ta nufi wajen motarta, d'aya daga cikin jami'an dake kula da mahaifinta ne ya taho shima a gadarance ya karb'i jakar hannunta da makullin mota ya nufi motarta dasu, dan in baiyi ba to masifa zaisha amma ba k'aramin d"aci ba abin ke mishi, har zata shiga mota taji saurayin nan yace "nine wawan?"

A wulak'ance ta juyo ta kalleshi tace "to da wa in ba kai ba? da wani ne wanda ya fika zama wawa a duniyar nan? ai kai kad'ai ne namijin dake zuwa gidan wacce yake ikirarin yana so kuma ya zauna zaman dirshan har da mik'e qafafu."

Nunashi tayi da yatsa tace "wallahi harka gama wa'adin daka dibarwa kanka ba zan tab'a kallonka a matsayin mutum ma bare harna fara tunanin soyayya da kai, désolé."

Tana fad'a ta shiga motarta ta bar gidan cikin matsanancin gudu, shi kuma taushe b'acin ranshi yayi da har yanzu yana ji a jikinshi zata iya zama tashi, a ranar da kuma hakan ta faru zata gane wanene shi.

Kafin ta fara gudanar da komai saida tasa masinger ya siyo mata fritte mai had'e da soyayyen nik'akk'en nama da jus d'in albasa da moutarde, tasa *Habiba* ta had'a mata kakkauran tea da zuma sannan ta fara wani sabon petis de jeûner d'in, tana fara ci Habiba ta sake shigowa cikin ladabi tace "madame, manager ne ke son ganinki."

Kallonta tayi a wahalce tace "uhum, kice ya shigo."

Juyawa tayi dan cika umarninta, takai wata lomar bakinta taji shigowarsu, amma jiji da kai yasa ta kasa koda kallonsu da ido, tsaye sukayi a kanta hakan yasa ta musu nuni da hannu akan su zauna, saida suka zauna sannan ta kallesu gaba d'aya ta kuma kalli manager tace "kai kad'ai aka ce kana son ganina, yana ganku ku biyu?"

"Eh madame, wannan shine wanda za muyi magana akan ci gaban daya kawo mana."

Sake kallon saurayin tayi wanda idonshi ke kan kallon yatsun hannayenta da take cin abinci dasu, jan lallen da suka sha da dogayen akaihu na kanti wanda suma ta lullub'esu da pink couleur d'in vernie, sosai suka birgeshi duk da dai ya tsani mai su d'in, maida kallonta tayi ga plate d'in abincinta taci gaba da ci har saida ta gama sannan ta d'auki bidon (gora) d'in ruwa ta zura hannunta ta tagar dake bayanta ta wanke hannu ta juyo da nufin aje bidon d'in ta d'auki lotus dan goge hannu.

  karaf idonta suka sauka akan gayen nan daya kasa d'auke idonshi akan kyakyawar hallitarta, da sauri ya d'auke idonshi tare da had'e fuska tamkar hadarin gabas, dan tunda ta fara aiki anan take tak'ama wajen mahaifinta ne ya lura tana da raini shi kuma ba zai d'auka ba, saida ta goge hannun ta tsaya ba yare data zauna ba ta kallesu tace ina jinku.

Hannu manager yasa a jaka ya fito da takalma ya mik'a mata yana fad'in "wannan shine sabon sanfarin da wannan ma'aikacin namu ya fito mana dashi, shine nace kafin muci gaba da bugawa sai mun samu izininki."

  Karba tayi bayan ya gama mata bayanin ta kallesu da kyau, tabbas sanfurin ya birgeta dan kuwa basu da maraba dana maza harda gidan babban yatsa, ga kuma tudunsu shima kamar dai na maza, ajesu tayi qasa ta cire na qafarta tasa wad'annan, su kam kallo suka bi qafar da ita yayin da saurayin ke ma qafar kallon qurilla wacce tasha jan lalle sai dogayen akaihu itama data saka masu kamar dai na hannuwa, ganin yanda suka zauna a qafarta suka mata kyau yasa ta cire ta zauna a kujerarta tace" kuje kawai ku ci gaba da bugawa, ku bar min wannan zanyi publié a Internet nasan zamu samu masu so.

Cikin farin ciki bayan sunyi godiya suka tashi zasu fita, muryarta ta tsayar dasu tace "fasahar waye?"

Post a Comment

Previous Post Next Post