Gunji Fassarar Algaita Dub Studio Indiyan Hausa

  GUNJI 1&2  (Algaita)

V.I.P India Hausa

 
Badariyya na zaune tana buga game taji land line din dakinsu na Kara, pause ta danna ta Mik'e tana tsaki, "hello. ta fadi cikin muryarta Mai cike da izza da isgili, hi Badar zo ki bude min kofa kuma kiyi a hankali Kar mummy ta jiki kin gane ko, katse wayar tayi ba tare da ta amsa shi ba ta juya ta fita daga dakin. 

  Dakin mummy ta nufa, bud'e kofar tayi ta shiga ba tare da tayi sallama ba, dan a ganin Badariyya sallama ta talakawa ce, hasken da ya gauraye d'akin ne ya farkar da mummy daga bacci, Mikewa tayi hade da mik'a tace "BADAR lafiya, yaya Musaddiq ne ya kira ni wai in bud'e mishi kofa.

Bawan Allah yana waje yana jiran Badariyya ta bud'e mishi kofa, ganin da yayi har minti 5 ta wuce bata bude ba ya fara mita cikin zuciyarshi, d'aga wayar yayi da niyyar sake kira yaji ana tab'a kofar, tura wayar yayi cikin aljihu ya k'arasa kusa da kofar fuskarshi d'auke da murmushi, "ina kika tsaya ne haka, har hakuri na ya fa maganar ta makale mishi a mak'oshi sakamakon ido hud'u da sukayi da mummy,
zaro ido yayi ya had'iye wani mugun miyau,
dariya ya fara yi yana fad'in mummy baki kwanta ba, tun d'azu Ina nan k'ofar gida a zaune ni da Tinau Mai gadi yana bani Labarin k'auye, sannan malam juyawa tayi ta barshi a tsaye,

Shigowa yayi ya rufe kofar ya bi bayanta da gudu, can gefe ya hango Badariyya tsaye tana mishi kallon raini, harara ya jefe ta dashi yace "tun kina yar ficiciya kin iya munafurci da makirci Ina ga in kin girma, wallhy kinji haushin rayuwar ki idiot, tsaki taja ta wuce d'akinsu, Kofar dakin mummy ya karasa, a hankali ya murd'a kofar ya shiga had'e da sallama, kusa da ita yaje yayi kneel down ya kamo hannunta yace kiyi hakuri mummy, wallahi ba party na je ba, ina gidan su Mahmud tun da na fita daga gida, sai dare na bar gidansu na dawo kofar gida na zauna, Dan Allah kiyi hakuri banason wannan fushin please ya karashe a shagwabe, bata tanka mishi ba ta zame hannunta cikin nashi tace "bani, zuciyarshi na dukan uku uku yace "me zan baki? 

K'ara tamke fuskarta tayi tace kud'in Baffa da na aike ka dashi, dakewa yayi yace "ni gidan mama suwaiba kika aikeni saidai ko driver kika aika gidan Baffa, 

"karka raina min hankali Musaddiq, 
kalleni da kyau banyi girman da zan fara mantuwa ba, dubu biyar na baka ka kaima "SUWAIBA" dubu d'ari biyu na Baffa, sai dubu Hamsin na k'anwar k'awata "Hajiya Nafeesa dake layin su suwaiba.


Haka Labarin Yacigaba ta

Bud'e baki yayi yace "Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun, mummy ai banji duk lissafin da kika min ba, ni dai sunan mama suwaiba kad'ai naji, na bata dubu dari biyu da biyar, ga dubu hamsin nan a aljihuna na manta inda kika aikeni dashi, karki damu gobe in shaa Allah da wuri zan kai mata, kika ce gidanta na kusa da gidan mama suwaiba ko?

Wani mugun kallo ta bishi dashi had'e da taune leb'enta, matsawa baya ya fara yi dan yasan in mummy ta fara taune leb'e to abin da zai biyo baya bazaiyi kyau ba, dai dai kofa ya tsaya kamar zaiyi kuka "yace mummy kiyi hakuri dan Allah, 

cike da takaici tace "Musaddiq Anya rayuwar da ka daukarwa kanka Mai b'illewa ce, 
ka zama almubazzari Wanda baisan darajar kudi ba. in ba iskanci ba me suwaiba zatayi da dubu dari biyu harda d'oriya, wallhy tun muna mu biyu da kai gobe kafin goma na safe kaje ka amso min kudi na, kuma ka tabbatar ka kaima Hadiza kanwar Hajiya Nafeesa kana ji na ko, gyad'a kanshi yayi fuskarshi da bata cika nuna fushi ba ta canza launi saboda tsananin b'acin rai, Takalmin kafarshi ya cire ya kwanta yayi ruf da ciki yana tunanin yadda zaiyi ya samu dubu d'ari biyu gobe ba tare da yaje gidan mama suwaiba ba.

Sai karfe daya ya yanke shawarar Kiran yayyenshi mata ya fad'a musu komai yasan a cikinsu bazai rasa Mai bashi ba..... 

Post a Comment

Previous Post Next Post