Kare ya Cinye Jari-ri Akasar China

 Akwai Matuqar Darasi A Cikin Wannan Dogon Rubutun Labarin Al-mara Daya faru a Kasar Sin wato (China)

    Karen Ya Kasance Mai Biyayya Sosai Ga Matar Wanda Haan Yasa Har Take Iya Barin Jaririnta Da Karen Idan Zata Fita, Idan Ta Dawo Ma Sai Dai Ta Tarar Da Yaron Yana Bacci Sosai Cikin Nutsuwa. 

Watarana Wani Mummunar Lamari Ya Auku Matar Ta Bar Jaririn Da Karen Kamar Yadda Ta Saba Ta Tafi Anguwa, Tana Dawowa Kawai Sai Ta Tarar Da Wani Lamari Mai Ban Razani, Ga Jini Kaca-Kaca Ta Ko Ina a ɗakin, Ga Kuma Jaririn Nata Bata Ganshi a Cikin Abinda Take Ajiye Shi Ba.

Dukkanin Diapers Na Jaririn Yayi Kaca-Kaca Da Jini Kuma Bataga Yaron Ba, Tana Cikin Wannan ɗimuwa Na Rashin Ganin Jaririn Nata, Sai Ga Karen Ya Bayyana Daga ƙarƙashin Gado Da Bakinshi Caɓa-Caɓa Da Jini Yana Lashe Harshe Kamar Wanda Yaci Wani Abun Daɗi. 

Nan Fah Kawai Zuciyar Matar Ta Yaddar Mata Cewa Karen Ya Cinye Mata Jariri, Ta Samo Sanda Ta Dinga Bugunshi Har Saida Ya Mutu. Sai Kuma Taci Gaba Da Neman Sassan Jikin Yaron Nata, Koh Zata Samu Saura. 

Sai Ta Leƙa Wani ɗakin Dake Cikin Gidan, Ta Samu Jaririn Yana Ta Wasa Cikin Kwanciyar Hankali, Ta Dawo ɗakin Nata Kuma Tana Duba ƙarƙashin Gado, Sai Taga Wani ƙaton Macijii Anyi Kaca-Kaca Dashi.

A Nan Fa Ta Gane Cewa Ashe Karen Nata Shine Yayi Kaca-Kaca Da Macijin, Yayi Faɗa Da Macijin Ne Domin Ya Kare Yaron Nata Daga Sarar Macijin, Amma Saboda Rashin Haƙuri Da Saurin Fushi Ta Kashe Karen Dake Mata Biyayya Kuma Ya Riga Ya Mutu Babu Yadda Za'ayi Ya Dawo.


MUYI TUNANI AKAN WANNAN

  1. Yaya Muke Zartar Da Hukunci Akan Mutane Da Munanan Kalamai ?
  2. Mu Kuma Yaɗa Qarya a Kansu Kafin Mu Samu Lokaci Mu Auna Yanayin Da Suke Ciki?
  3. Sau Nawa Muka Jumping Into Conclusions Akan Wassu just Kawai Saboda Yanayi Na Shigarsu? 
  4. Mutane Nawa Muka Mayar Abokan Gabanmu Kawai Saboda Munji Ance "Sun Ce", "Sun Yiii", "Su Ne" Ba Tare Da Munyi Bincike Ba?
Koda Yaushe Mu Zamto Masu Haƙuri Kafin Mu Zartar Da Hukunci Akan Wassunmu Domin Gudun "Dana Sani" Kada Ya Zama Kalmarmu Ta ƙarshe.

Muna godiya da kasancewa damu Akodayaushe, Acikin wannan shafin namu..

Post a Comment

Previous Post Next Post