YAN BINDIGA SUNKASHE MAKIYAYA A JAHAR TARABA
Da Dumi Duminsa: A Jahar Taraba Yanbindiga da ba'asan ko suwayen bah sun kashe makiyaya Fulani da Sullu6awa har goma sha biyu, wassu kuma sun 6ace a daji.
Taraba Social Media Crew Initiative tayi tattaki zuwa inda abun ya auku agarin Zude gunduman Pangri dake karamar hukumar Bali na Jahar Taraba ran Uku ga watan Oktoba 3/10/2022.
Ado Abubakar Presidor wadda nakasance wurin daukar rahoton don ganewa ido irrin wannan munmunan lamarin.
Saurari takaiceccen hirar da nayi da Daya daga cikin wadda aka kashewa Yan Uwa.Y ayin daukar gawarwakin Taraba Social Media Crew ta dau hotuna.
Alh.Umar Bello Shugaban Kungiyar Kautal Fulaku na Jahar Taraba ya kasance a Bali don ganewa idonsa da jajantamusu irin wannan mummunar Aika Aika.Shugaban Kungiyar ya janyo hankalin Gomnati da jami'an tsaro ganin an zakulo wadda sukayi wannan mummunar Aika Aikan daga Karshe yayikira ga wadda abun yashafa da suyi hakuri, zasuyi iya kokarinsu ganin sunbiwa kowa hakkinsa.
Yanzu haka mutane hudu suna hanun jami'an tsaro inda Yan sakai suka kama.