Sabuwar Fassarar Algaita Dub Studio 2022 Indiyan Hausa

 Fassarar Algaita Dub Studio

   Bishiyoyin dogon yaro ne guda shida dasuke zagaye haka a dajin da ba datti alamun ana gyara wajen, kowani bishiyan an makala shooting target vector ajikinshi sai wani babban dan table haka dake filin wajen daba komi akai, jiinnjinjinnn karan power bike yacika wajen, daga kai nayi danna kawo muku rahoto da kyau.

  Daga dan nesa da bishiyoyin black power bike din ya tsaya batare da an kashe machine dinba sai kuka machine din yake mai kara as usual irin na power bike dinan, daga kafa nafara kallon mutumin kan bike din, black hermes covershoe ne akafanshi dake sanye da bakar safa, yasaka bakin straight leg trim trouser, sai black Versace greco hoodie ne ajikinshi, hannunshi sanye cikin wani irin hadadden black safan hannu na maza, bayanshi goye dawani hadadden black bagpack, ahankali ya daura hanun akan key machine din ya juya hakan yasa machine din ya mutu, da kafarshi na haggu ya taba break din machine din ya tsayar da ita da kyau kafin yay wani irin tsalle ya dirgo daga kan machine din ya.

   Tsaya yana wani irin jan rigar jikinshi yana gyara tsayuwa, dogone sosai cikakke dan yacika kayan dayasa fam, duka hannayen shi ya daga ya daura akan hamlet din dake kanshi, ahankali ya cire ya rike a hannu yana jujjuya hamlet din yana kallo, gabaki daya kanshi da fuskarshi nacikin wani irin safar fuska baki ya sanya wani irin bakin glass dake manne ido sosai irin wanda sojoji ke sawa, baka hango bakinshi baka ganin hancinshi sai tudun hancin da dan raga raga ta wurin hancin.

  Ajiye hamlet din yayi akan power bike din, ya daga hannunshi na haggu yana kallon screen din wani hadadden agogon dake daure a wutsiyar hannu akan safan hannunshi, sakin hanun yayi ya tura a aljihun wandon jikinshi dayan hanun kuma na lilo ya juya yafara tafiya kaman zaki yay wajejen bishiyoyin, awajen table din tsakiyar wajen ya tsaya yana bin bishiyoyin da wurin da kallo kafin sauke ya jakar bayanshi ya daura akan table din, zage zip din jakar yayi yaciro wasu bindigogi guda biyu kirar berreta M9 yana dan jujjuya su kafin ya gyara zaman su ahanunshi ya fara tafiya kaman zaki har yakai wajejen bishiyoyin.

  Gyara zaman shooting vector din daya daga cikin bishiyoyin yayi kafin ya juyo ya dawo ya tsaya agaban table din, gyara zaman bindigar yayi ahanunshi yana kallon shooting target vectors dake jikinshi bishiyoyin wurin tacikin bakin glass din dake kan fuskarshi, ahankali ya ijiye bindigar ya tura hanunshi cikin jakar yaciro earmuff, saka earmuff din yayi suka rurrufemai kunne kafin yadau daya daga cikin bindigogin ya saiti target din vector din, pulling trigger yayi yay harbin bindigar tai kara bam aiko ya sami target din daidai, kara saita bindigar yayi yacigaba dayin harbinshi kara kawai ke tashi adajin, saida yay kusan one hour kafin ya hada komi ya maida jakan ya sake kallon agogon hannunshi sanan yadau jakar ya goya, yatako dawanan tafiyar kaman zaki yahau kan bike din yatada dawani irin azababben gudu yabar wajen.

Gaban wani babban gida anan cikin dajin yay parking wani irin dirowa yayi daga kan mashin din yay cikin gidan, babban gidane sosai ga manya manyan mota daban daban a compound din, gakuma babban masallaci ata gefe, wani babban part yabude kofa ya shiga.

Post a Comment

Previous Post Next Post