Sabuwar Fassarar Sultan Fassarar Indian Hausa film 2022

   YANKAN KARFE 1&2 (Sultan)Kutsaya Ku Karanta Wannan
 
    Babban compound ne sosai dake dauke da shuke shuke da bishiyoyi masu daukar hankali, kai kana ganin tsakar gidan kasan naira ta xauna, makeken tsakar gidan na dauke da sassa har uku masu fenti iri daya, ko wani sassa kuma akwai tazara mai tsayi tsakaninsa da wani sassan, sashin farko wanda shi xaka ci karo da bayan shigowar ka gate din xamanin dake babban gidan ba dai girma ba don sashin duk ya fi sauran girma, duplex ne babban gaske sai parking space gari guda dake gefe. 

   Durkushe a bakin tap dake babban sashin farko wata farar budurwa ce da baxata wuce shekaru sha takwas ba, duk da a duke take hakan baxai sa aki gane doguwa ce ita din ba, ruwan tap din na ta xuba bucket din da ta tara don ya cika, sai shafa socks din hannunta take kamar mai tausayinsa, daga ves, huluna sai socks kala uku sune kayan da take wankewa a wajen amma ta kusa awa daya, kofar entrance da ta ji an bude ya sa ta kamewa daga inda take durkushe lkci daya ta xaro ido gabanta ya fadi don ita dai a iya saninta babu kowa sashin banda ita da ke wanki tun daxu, occupant din bangaren duk sun tafi biki ta kuma ga fitarsu, wanda da ace suna nan tasan ko hauka take baxata fara xuwa bangaren su tayi wanki ba, a hankali ta juya don ganin wanda ya fito, wani matashi ne dogo sosai wanda baxai haura shekaru talatin da uku ba tsaye dai dai entrance din shiga gidan sanye da jallabiya milk color, 
   
     Ta dauke kai tana ci gaba da daurayenta, ya rungume hannuwan sa calmly yace "Keee" kamar xata yi kuka ta juya ta kallesa, yace "Me ya kawo ki wanki nan?" Ta buda manyan idanuwanta tace "Tap din mu fa ne ya lalace jiya kuma....." Ya katse ta yace "Tashi ki bar wajen" Tace "To ai na kusa gamawa fa" strictly yana d'an daga murya yace "Kwashe kayan ki ki bar nan kar ki yarda in iso inda kike" ta dauke kai hade da turo baki ta mike ta xubda ruwan gaba daya ta hade buckets din bayan ta xuba yan kayan da ta wanke ciki ta kwashesu gaba daya ta bar wajen kamar xata tashi sama ba tare da ta sake kallon inda yake ba.
Ta murguda baki bayan tayi nisa, murya can kasa tace "Allah ya isa" Dai dai part na biyu da ya kasance wani babban hadadden Bungalow ta tsaya, shi ma kuma bangaren na da nasa parking lot din da xai dau motoci uku, ta dinga kallon sauran kayan da bata gama wankewa ba kamar xata yi kuka, to ita yanxu ya xata yi da su.   
Ammi na ganin bata gama ba sai ta fara mata fada yanxu tace tun daxu me take, kallon hanyar da xata bi xuwa part din karshe tayi, ta tabe baki sanin ba lallai ma mai sashin ta bar ta ta ta6a mata tap ba, tana ta tsaye can kuma dai ta wuce can bangaren karshen, shi ma sashin bungalow ne sai dai bai kai nasu ba, tsarin ma ba iri daya bane, a hankali ta ajiye buckets din hannunta dai dai tap din dake opposite entrance din shiga parlor tana yi tana satan kallon kofar, cikin dubara ta bude tap din yanda xuban ruwan bazai yi kara ba, ta tara bucket din a karkace kar ma aji xuban ruwa ta ci gaba da daurayenta, sosai gabanta ya fadi jin taku duk a tunaninta mai bangaren ce, mutumin daxu ne ke tahowa bata yarda sun hada ido ba ta ci gaba da wankinta, ko kallon inda take shi ma bai yi ba, bai kuma kai ga shiga parlon ba suka ji muryar wata tsohuwa tana cewa.
     
    Ni wai ya nake jin kamar ana taba min pampo a wajen nan ne" da sauri ta kashe tap din ruwan xata kwashi kayanta ta gudu sai ga tsohuwar ta fito, Sake baki tayi tana kallon ta kafin tace "Waye kuma wannan, meye kike min kusa da pampo?" Budurwar ta turo baki tace "To inna namu ya lalace..." Inna ta katse ta da sauri tace "Da ya lalace ni na lalata maku?" Budurwar tace "To wai ma ba daxu kika ce in xo in debo maki ruwa in kai maki bayi ba, shine fa na zo xuba maki" Inna na mata wani kallo tace,
Ke din? Ke din da na sani ce xaki kai min ruwa bayi munafuka? bayan ba Aisha sunana ba, to wllh ki kiyaye ni a gidan nan ruwana ba na banxa bane kar ki sake xuwa min nan, kin lalata naku nima ki xo ki lalata min nawa saboda mugunta koh, to uwar ki ce xata debo mun ruwan idan na tankin ya kare, haka kawai ki bar ni da diddigin pampo duk tsutsa cuta ta kama ni in bar 'ya yana da wahala.

   ke dai wannan yarinya ta Bukar muguwa ce wllh, shegen barnar ki ta fi karfin ki, to wane 6era ma" ita dai Budurwar sai kallon ta take kamar xata yi kuka, inna na xaro ido tace "Maxa dau min ruwana ki tafi ki juye min a bandaki, ni dai a gidan nan duk wanda ya diba da hakkina gaskiya ban yafe ba tunda abun haka ne, don kowa sai da aka dasa masa pamponsa amma don mugunta sai ku wani kwaso shegun bokitan ku duk datti kuna kwashe min ruwa mugayen yara" Ita dai tana tsaye wannan karan ta daure fuska sai kallon ta take.

A fusace inna tace "Baxa ki je ki juye min a bandaki ba ko sai nasa an kira min Bukar ya taho duk inda yake yanxu?" Daukan ruwan Budurwar tayi fuuuu ta wuce ciki, inna ta shiga parlor ta dauko wani karamin kwado ta kulle tap din ta wuce cikin parlor tana cewa "Gwara in ta tsayawa ba ruwan nima da a xo ana ta debe min a cuce ni" Tana shiga parlor ta kalli matashin dake xaune kan kujera yana danna wayarsa, ta hade rai ta dau kyallen da take goge goge ta ta fi gun kayan kallo ta ci gaba da gogenta tana cewa "Ka sake dawowa karasa sauran fitsarar da ka mance baka yi ba kenan, wato duk wanda kayi jiya bai isheka ba, to ni dai a fita a bar min parlor ba ruwana, ba katon banxan da zan kula yau ta kaina nake, kaje can kayi ma uwar ka" shi dai bai tanka ta ba sai danna wayarsa yake, Bayan wani lkci ya mike yace "Dama Abba ne yace in xo in baki hakuri" daga haka ya nufi kofa fuska daure, da karfi Inna tace "Imaan tunda mutumin nan ya shigo kinji ya ce min wani abu?? To ni dai ba ni ka ba hakuri ba wllh, idan kuma ba ka yi hankali ba sae in iya fitar har ofis in sami Ahmadu ynxu.
  
  Imaan ta rufe babban roban da ta jawo daga karkashin gado tana kokarin daure alkakin da ta cika a leda jin inna ta sake kiranta tace "Gani nan xuwa" window ta bude a hankali ta jefar da ledan ta shiga bayi ta wanke hannunta da sauri ta fito ta shiga parlor fuska daure tace .

Post a Comment

Previous Post Next Post