Baya iya barci Adakin da Babu Hoton Buhari Acikin ba : Nigeria

 Mutumin da ba ya iya kwana a ɗakin da ba hoton Buhari

Usama Yarima, mazaunin ƙaramar hukumar 'Yan kwashi a jihar Jigawa a arewacin Najeriya ya ce tun yana ƙarami ba ya iya kwana a ɗakin da ba ba bu hoton shugaban ƙasar Muhammadu Buhari, sakamakon irin soyayyar da ya ke yi wa shugaban ƙasar.

Ya ce bai taɓa zuwa makarantar boko ba amma sakamakon soyayyar da yake yi wa shugaban ƙasar ta sa ya koyi karatun boko.

Usama ya haddace duka ƙananan hukumi 774 da ke fadin Najeriya, duk da a cewarsa bai taɓa zuwa ko da ƙaramar hukumar da ke makwabtaka da tasa ba.

Ya shaida wa BBC cewa babban burinsa shi ne a taimake shi a saka shi a makarantar boko kasancewarsa mai ƙaramin ƙarfi.

Post a Comment

Previous Post Next Post