Matashiyar da ke fafutukar maza su rinka kara aure - Kannywood

Zainab Umar, mai shekara 25, na fafutukar maza masu mace daya da su kara aure saboda a cewarta "mata sun fi maza yawa".

Zainab Umar ta shahara a kafafen sada zumunta wajen wannan fafutuka

Matashiyar wadda 'yar asalin jihar Adamawa ce ta ce "duk da cewa mahaifiyata ita kadai na taso na gani a gidanmu amma wannan ba zai hana ni fafutukar da nake ba."

Ta kara da cewa "ni yanzu ban yi aure ba amma kuma ba zan iya auren mara mace ba. Kuma a yanzu haka a matsayina na budurwa zan iya auren mai mace uku na zama ta hudu."

Zainab ta ce tana mamakin matan da suke hana mazansu kara aure "alhali kuma mazan na bin wasu matan a waje", ni abin da ba na so kenan wato 'kishiyar waje.

Post a Comment

Previous Post Next Post