Da taimako mawaki Rarara ya kame zukatan yan uwansa mawaka da yan wasan Hausa (Kannywood).
Babu mai taimakon yan uwansa mawaka da yan wasan Hausa (Kannywood) a kasar nan kaf kamar Rarara..
Duk wani mawaki ko dan wasan Hausa da yake a halin ni 'yasu ko yanayin kunci na rayuwa,matukar Rara yana sane to kuwa yana taimaka masa da abinda zai rage radadin rayuwa.
A hotunan da kuke gani mawakin ne yakai ziyara ga mahaifiyar marigayi Rabilu Musa Ibro, wanda abokine ga Rara lokacin yana raye, bayan rasuwar Ibro Rara ne ya janyo Dan-dan Ibro zuwa harkar film matuka ta hanyar bashi damar fitowa a wasu fina-finan da har yayi shura a yanzu
haka zalika mawaki Rara ya janyo diyar marigayi Ibro zuwa harkar film da waka,Ummi Ibro bayan taka rawa a harkar Film mawakiya ce da Rara yake sakata a rukunin mawakan da suke wake yan siyasa musamman a wasu wakokin Rarara zakuji da ita a mawakan.
Halin kyautatawa da Rarara yake dashi,shine musabbabin matukar kauna da mawaka ko yan wasan Hausa suke masa.Menene Ra'ayinku Dangane da wannan
Shiga Bangaren comments domin kusamu Daman yin Sharhi
Tags:
Kannywood