Ya Sarrafa Kashin Shanu Izuwa Gas- Wani Dalibin HND a Kebbi- Arewacin Nigeria

 Da dumi dumin sa!!!!

Wani Matashin Dan Makarata Ya Sarrafa Kashin Shanu Izuwa Iskar Gas

   Kamar yadda kuke gani wani dan Jahar Kebbi state ne daga karamar hukumar mulki ta Danko Wasagu L.G.A Musa Lawal Wasagu (Na Gwaggo)

Dalibine a makarantar makarantar Waziri Umaru federal polytechnic Birnin kebbi ya sarrafa kashi/tutun shanu ya koma gas ta yadda za a dafa abinci cikin sauki.

   Yayi wannanne ashekarassa ta karewa a mataki na HND | Al'ummar Danko/Wasagu tayi farin ciki da samun jajirtaccen matashi kuma mai hazaka, Allah yakara basira Amin.


    Muna kira ga gwamnatin jahar kebbi mai adalci kuma mai tausayin talakawanta da ta dubi wanga bawan Allah da idon rahama domin atallafa masa ta yadda zai kawoma alummar jahar kebbi cigaba.

   Mai Girma Gwamna Sen Abubakar Atiku Bagudu muna yimaka murna da samun wannan ci gaba.

   Haryanxu Akwai Masu Basira da Hazaqa dakuma baiwar Kimiyya da Fasaha A Africa musanman ma a Nigeria, Yakamata Ace masu Hannu da Shuni ku tari ku karfafa Wainna masu baiwar Tunda Gobani bazatayi ba, Saboda Kar Adunka yin Asaransu batare da Duniya Taco Amfaninshi ba, Karda Baiwarsu ta tafi Abanza, 

  Saboda Akwai lokutan da za'a iya nemonsu Arasa, Duk Matashin Mai gurin yayi wani Abun Fasaha yaga Ana Kyalesu Babu wani Taimako Hakan Zaisa su Gajiya su safe wajen habbaka baiwar tasu, Wannan Shawarane dazata Amfani Kasarmu Nigeria Baki daya, Mugudu Tare Mutsira Tare, Muci Moriyar Junanmu da Fasahohinmu, 


Source: Nafiu Benawa 

SA Media Chairman D/Wsg L.G.A

31/10/2022.

Post a Comment

Previous Post Next Post