ce-ce-ku-ce kan kirkiro ofishin 'babbar 'yar shugaban kasa

 Yan kasar Kenya da ke amfani da shafukan sada zumunta sun bayyana kaduwarsu bayan da suka fahimci cewa an kirkiro ofishin 'yar shugaban kasa William Ruto.

A wani bidiyo da ya karade shafukan intanet, an ga 'yar shugaban kasar ta biyu, Charlene Ruto tana yin jawabi a wurin wani taro a Tanzania inda ta gabatar da "tawagarta daga Kenya” ciki har da mai ba ta shawara da kuma wani wanda shi ne “shugaban cinikayya da zuba jari a ofishin 'yar shugaban kasa".


Mahalarta taron sun yi shewa da tafi lokacin da ta bayyana tawagar tata.

“Ban san abin da ya ba ku dariya ba,” a cewar Ms Ruto a yayin da take mayar da martani kuma take kokarin ci gaba da gabatar da tawagarta

A dokokin Kenya babu ofishin 'yar shugaban kasa kuma ba a fitar da wata sanarwa ta kirkiro ofishin ba

Yan kasar Kenya da ke mu'amala da shafukan sada zumunta sun yi ta caccakar abin da suka kira amfani da harajin 'yan kasar ta hanyar da ba ta kamata ba.

"Charlene Ruto ta gabatar da tawagarta daga ofishin 'yar gidan shugaban kasa wadanda ake biyansu da harajin 'yan kasar duk da cewa samar da ofishin ya haramta," a cewar wani dan kasar Kenya da ke amfani da Twitter.

Wani kuma ya yi tambaya kan yadda aka kirkiri ofishin sannan ya watsa bidiyon bayanin 'yar gidan shugaban kasar:

Ms Ruto tana yawan ganawa da shugabanni a fadin kasar kuma tana halartar tarukan kasashen duniya tun bayan da mahaifinta ya zama shugaban kasa.

Tana cikin mutanen da aka fi magana a kansu a shafukan intanet ranar Laraba.

A baya ta jawo ce-ce-ku-ce saboda yadda take tsoma baki a harkokin siyasa - inda aka sanya mata suna Quickmart Ivanka a shafin Twitter, wani shagube da ke nuna kamanninta da Ivanka Trump, 'yar tsohon shugaban Amurka Donald Trump

Post a Comment

Previous Post Next Post