Tirkashi- Babu Wani Ribar Aure: Inji Sabuwar Matashiyar Kannywood

 Babu Wata Ribar Azo Agani A Cikin Aure Inji 'Yar Gwagwarmaya Zainab Naseer Ahmad

Yayin da yawancin lokuta iyaye ke Alla-Alla su sanya yayan su mata dakunan mazajen su domin gujewa sharrin zamani da kuma lalacewar tarbiyya, sai gashi wata matashiya mai amfani da yanar gizo da ake Kira Zainab Nasir Ahmad, tace mutane ne kawai ke zuzuta aure kai kace akwai wata babbar nasara a cikin sa, sai dai a zahirin gaskiya wannan tunani shirme ne kawai hasalima babu wani abun azo a gani a cikin sa.

Tace "mutane sai suyi ta zambatar yarinya idan takai matakin aure kuma batayi ba, wannan dalili ne yasa sai kaga wasu mazan ma na tunanin kamar alfarma sukayi miki in suka tunkare ki da zummar aure.

A cewar ta, "shifa aure abu ne daya kacal na rayuwa, kuma ba kowa ne zaiyi shi ba, tace a gaskuya ya kamata a daina musguna musu akan cewa wai lallai sai sunyi aure.

Ta kuma kara da cewa, ba kuma wai don mace tayi aure hakan na nufin cewa tafi wadanda basuyi bane, duk daya suke.

Daga karshe sai ta kara jaddada cewa ba shakka babu wani abun azo a gani a cikin aure.

Menene ra'ayinku akan hakan?

Ku Kalli Video 👇👇👇👇Mungode da kasancewa damu


Post a Comment

Previous Post Next Post