Acikin shafin Facebook na ga gawar mahaifina an Posting da Sharing


 Lokacin da wani dalibi ɗan ƙasar Habasha Moti Dereje ya shiga shafinsa na Facebook a ƙarshen watan Nuwambar 2018, ya yi tsammanin ganin irin abubuwan da ya saba gani daga abokai da 'yan uwa.

Maimakon haka matashin ɗan shekara 19 da ke karatu a Addis Ababa babban birnin ƙasar sai ya ci karo da abin da ya rikita rayuwarsa.

"Ina shiga domin ganin labarai, sai naga gawar mahaifina a yashe a ƙasa," haka matashin ya shaida wa BBC.

Ba Moti ne kadai ya kaɗu da ganin wannan mummunan hoto ba, amma dai a haka ya gano cewa an kashe mahaifinsa.

"Ƙame wa na yi a lokacin. Abin ya girgiza ni matuƙa,'' ya ƙara da cewa.

Moti Dereje riƙe da hoton mahaifinsa, da kaninsa a lokacin suna yara

Yayin da Habasha ke fama da rikicin siyasa tsawon shekaru, kafafen sada zumuntar ƙasar cike suke da munanan hotuna da hotunan bidiyo, labaran ƙarya da kuma na tunzura mutane da ke tayar da rikici.

Masu fafutuka sun daɗe suna kiraye-kirayen a riƙa tace abubuwan da ake wallafawa a kafafen kafin su janyo wani rikicin.

Shi kuwa Moti maimakon ya ga an cire hoton mahaifin nasa, sai ma ƙara ganin hotuna irin waɗan nan da yake yi.

Mahaifinsa wanda tsohon ɗan majalisa ne, kuma yana aiki da jami'a, yana daga cikin 'yan siyasar da ake neman kashewa a yankin Oromia.

Yankin ya rika fuskantar tashe-tashen hankali, a lokacin da ake yawan samun kashe fitattun mutane.

"Kamar ma farin cikin kashe shi suke yi. Abu ne mai matukar raɗaɗi," in ji Moti.

BBC ta ga waɗan nan hotuna guda 15, wanda Moti ya ce ya kai kokensa ga Facebook domin su cire su.

Hukumomin Faceboook sun yi alƙawarin cewa idan iyalai a ƙasar suka shigar da ƙorafi kan hoto mai tattare da tashin hankali za su cire shi.

Sai dai Moti ya shigar da koken bai san adadi ba cikin shekara hudu kuma har yanzu ba a cire ba.

Ba a mayar da hankali kan abubuwan da ake sawa a Habasha'

An rika nuna damuwa kan yawan hotunan da ake yaɗa da kuma maganganun ƙiyayya da ake yawan wallafawa a shafukan sada muzunta.

Wannan matsala ce gabanin 2020, amma lokacin da aka fara yaƙin yankin Tigray a watan Nuwambar shekarar, yawan hotunan da dake wallafawa na rikici sai ya riƙa ninninkawa cikin sauri.

A 2021, hukumar kamfanin Facebook ya ce zai yi bincike musammam a Habasha kan yadda ake wallafa hotuna da bidiyo na ƙiyayya da suke ƙara wa rikicin wuta.

Amma fa babu wani bincike da aka gudanar mai kama da hakan.

BBC ta tambayi Meta kan me ya hana gudanar da bincike, kakakin kamfanin ya ce za a yi hakan saboda take haƙƙin ɗan adama a Habasha.

Masu sharhi na cewa mutane suna amincewa da abin da suke gani a shafukan sada zumunta, kuma ko da an tsara abin ne domin ya haifar da rikici.


A bara an sanar da cewa an shigar da ƙarar kamfanin Meta, wasu mutane biyu 'yan Habasha ne suka shigar da ƙarar kan cewa alƙaluman da kamfanin ke saki suna ƙara ta'azzara rikicin.

Meta ya ce sun zuba manyan kudi domin lura da yadda ake cire abubuwan da aka wallafa a shafin.

Amma wata kwararriya wajen tabbatar da labaran ƙarya Rehobot Ayalew, ta yi tambaya kan cewa me kamfanonin d suka mallaki kafafen sada zumunta ke yi domin shawo kan matsalar.

"Ba na tsammanin kamfanonin suna mayar da hankali kan Habasha," in ji ta. Yana ɗaukar dogon lokaci kan a cire wani abu da aka wallafa da bai da ce ba".


Tsananin bacin rai

Ms Rehobot ta kafa hujja da wani bidiyo da aka riƙa yaɗa wa a watan Maris ɗin 2022, wanda aka ƙona wani mutum ɗan yankin Tigray a raye.

"Da farko na'urar da aka sanya mai amfani da irin tunanin mutane ya kamata ta cire shi," kamar yadda ta yi bayani.

"Bayan an yi koke a kansa, ya kamata a ce an cire shi cikin gaggawa, amma duk da haka sai da ya kwashe awanni."

Yanzu dai ɗan shekara 23 Moti na shirin ci gaba da rayuwarsa a matsayin mai daukar hoto da bidiyo, da muka shirya shiri na musamman game da abin da rayuwa ta koya masa.

"Ina ganin lokaci ya yi da zan faɗi labari na, idan na yi nasara to zai zama wani sauyi da zan yi alfaharin ne na kawo shi," in ji shi.

Yace waɗan nan irin hotuna za su ci gaba da damunsa har sai ranar da aka fara kawo karshensu.

"Duk lokacin da naga an wallafa hoton gawa a Facebook kan yaƙin Habasha, sai in ji hankalina ya tashi. Wannan ka iya sanya mutane tashin hankali, kamar dai yadda ya faru da ni.

"Abin na tayar min da hankali."


Kalli Cikakken Video Kaitsaye 👇 Anan👇


Post a Comment

Previous Post Next Post