Ibtila’i: An Tsinci Gawar Ɗan Takarar Gwamna A Mace a Jihar Imo

 Alfijr ta rawaito Wani dan takarar jam’iyyar Labour a zaben fidda gwani na gwamna da za a yi a jihar Imo, Cif Humphrey Anumudu an tsinci gawarsa a gidansa.

Dan takarar ya rasu ne a gidansa da ke Legas bayan ya dawo daga taron LP a hedikwatar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja ranar Juma’a.

Wani dan asalin masarautar Mbieri da ke karamar hukumar Mbaitoli a jihar Imo, an samu rahoton gawarsa Anumudu a gidansa a wani abin da majiyar ‘yan uwa ta bayyana a matsayin “Mutuwar Fuju a.”

A matsayinsa na hamshakin attajirin dan kasuwa ya kasance dan takarar gwamnan jihar tun 1998.

An ce shi ne ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a jihar a shekarar 1998 kafin a bai wa Achike tikitin takara.

Udenwa wanda ya ci gaba da mulkin jihar a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007.

Tun a lokacin ya ke tsayawa takarar kujera ta daya a jihar a 2019 ya kasance dan takarar gwamna na jam’iyyar Labour ta Zenith.

Marigayi dan siyasar ya riga ya biya Naira miliyan 25 don neman takarar Gwamnan Jihar Legas a ranar 11 ga Nuwamba 2023.

Cif Anumudu, kwararre a fannin shari’a kuma hazikin dan siyasa, shi ne kuma babban jami’in gudanarwa na kamfanin Globe Motors.

Ya tsaya takarar Gwamna a baya a karkashin jam’iyyar All Progressives Grand Alliance.


Kalli Cikakken Video Kaitsaye 👇 Anan 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post