Matafiya 21 Sun Rasu Sakamakon Haďarin Mota A Jigawa, Inda Suka Kone Ķùŕmùś yanzuhaka suna jibge a asibiti ana cigiyar 'yan uwansu

 R.I.P 😭 Matafiya 21 Sun Rasu Sakamakon Haďarin Mota A Jigawa, Inda Suka Kone Ķùŕmùś yanzuhaka suna jibge a asibiti ana cigiyar 'yan uwansu

Kai tsaye daga asibitin Kwanci dake cikin garin Hadejia a jihar Jigawa, inda ake jana'izar wasu matafiya da suka rasu sakamakon hadarin mota tare da konewa kurmus su 21 a hanyar su ta zuwa garin Maiduguri jiya Alhamis.

A halin yanzu akwai wanda har yanzu ba a gane hotunan su amma duk wanda Allah ya sa ya san 'yan uwansa sun yi tafiya zuwa garin Maiduguri jiya Alhamis to sai ya garzayo zuwa asibitin domin tantance dan uwansa.

Za a dan jinkirta zuwa wani lokacin idan Allah ya sa ba a gama samun 'yan uwan su ba, to za a hada su baki daya a yi musu sallah, sai dai a yi musu addu'a Allah ya yi musu rahama. Allah ya sa sun huta.

Kalli Cikakken Video Kaitsaye Yadda Ake Zakulo Gawawwaki da Maraunata Acikin Motocin Dasukayi Hatsarin 👇 Anan 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post