Police Kano Sun Kama ɓarayin Babura Da ƴan Fashin Waya A Kano Acikin Watan Ramadan yau 31/3/2021

 Ƴan Sanda Sun Kama ɓarayin Babura Da ƴan Fashin Waya A Kano

Rundunar ƴan sandan jahar Kano, bisa jagorancin kwamishinan ƴan CP Mamman Dauda ta yi nasarar cafke mutane 14 da ake zargi da aikata laifin satar Babura masu ƙafa biyu ,Adaidaita sahu da kuma ƴan fashin waya da Dilolin ƙwaya.

Kakakin rundunar ƴan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Alhamis a birnin Kano.

Sanarwar ta ce kamar yadda babban sifeton ƴan sanda na ƙasa IGP Usman Alƙali Baba ya bayar da umarnin yin aikin tsaro da al'umma da kuma faɗaɗa sintiri a faɗin jahar ne aka samu nasarar kama mutanen.

" daga fara Azumi zuwa wannan rana, mun yi nasarar kama manyan masu laifi mutane 14 da laifuka kamar, fashi da makami suna ƙwacen wayoyin jama'a, Dilolin ƙwaya da kuma masu kwacen baburan Adaidaita sahu" SP Kiyawa".

Rundunar ta samu nasarar , dawo da Babura masu ƙafa biyu guda 2 , Adaidaita sahu 3, da kuma kama Allurori da ƙwayoyi da matasa ke yin amfani da su, wajen aikata laifin bayan sun bugu.

Daya daga cikin waɗanda ake zargin mai suna Bala Muhammad Hotoro , ya bayyana cewa an kama shi da laifin satar Babura masu ƙafa biyu , kuma abaya an taɓa kama shi da irin laifin har aka gurfanar da shi agaban kotu aka yanke masa hukunci , bayan ya kammala zaman gidan yarin ya ci gaba da aikata laifin.

Mansur Hamisu Abdullahi Ja'en ya shaida wa jami'an ƴan sanda yadda suke ƙwacen wayoyin jama'a ta hanyar tsoratar da su da Wuƙaƙe.

Shima Yusuf Yahya Ɗorayi da yake ɗaukan masu ƙwacen wayar a cikin Babur ɗin Adaidaita sahu , ya bayyana cewa ya kai shekara guda yana tuƙa masu ƙwacen wayar , wanda idan an kammala an siyar sai a bashi kason sa.

A ƙarshe Kiyawa ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da su a gaban kotu dan su fuskanci hukunci.

Kalli Cikakken Video Kaitsaye 👇 Anan 👇

ATP Hausa TV Ibrahim Al'amin Makama

Post a Comment

Previous Post Next Post