An Ragargaza Baburan Talakawa ’Yan Acaba 476 Da Aka Kwace A Abuja

 Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja (FCTA) a ranar Laraba ta ragargaje baburan da ta kwace daga hannun ’yan acaba kimanin 476.

Hukumar ta kuma sha alwashin ci gaba da nuna ba sani ba sabo a kan tabbatar da bin dokar hana acaba a birnin, duk kuwa da irin hare-haren da ta ce ana kai wa jami’anta.

Daraktan Sashen da ke Kula da Hanyoyi na hukumar, Abdullateef Bello ne ya sanar da hakan lokacin da ya jagoranci ragargaza baburan a unguwar Area 1 da ke Garki a birnin.

Ya kuma lashi takobin cewa za su ci gaba da aikin lalata baburan matukar masu amfani da su suka ci gaba da yin kunnen uwar shegu da dokar.

Daga nan sai ya bukaci sauran al’ummar gari da su taimaka wa hukumar a kokarinta na tabbatar da cewa ana ci gaba da bin dokar sau da kafa.

Shi ma da yake jawabi, Babban Hadimin Ministan Abuja a ka sa’ido, duba aiki da tabbatar da bin doka, Ikharo Attah, wanda ya duba aikin lalatawar, ya ce suna nan tsaye a kan bakarsu ta ci gaba da aikinsu matukar masu karya dokar ba su daina ba.

Ya kuma nuna mamakinsa kan yadda duk da gargadin da aka sha yi ta kafafe daban-daban, da kuma yadda aka lalata babura sama da 1,000 cikin ’yan watannin da suka gabata, har yanzu mutane ke ci gaba da yin kasadar kai baburan wuraren da aka haramta.

Kalli Video Yadda Ake Rugurguza da Markade Baburan Yan achaba Kaitsaye 👇 Anan 👇
Post a Comment

Previous Post Next Post