Kotu Ta Ɗaure Wani Mai Damfarar Ɗaukar Mutane Aiki A Jihar Kano

 Babbar Kotu a jihar Kano ƙarƙashin Mai shari’a Hadiza Suleman ta sami wani Ahmad Sultan Sardauna da laifin haɗa baki da kuma samar da takardun jabu inda kuma ta yanke masa hukuncin shekara huɗu a gidan gyaran hali.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Sultan gaban kotun tare da Emmanuel Tunde a watan Nuwamban bara saboda yin jabun wasu takardu a yunƙurin damfarar wani ɗan Somali kuɗi $4,661 da sunan nema masa aiki a Majalisar Ɗinkin Duniya.

Emmanuel dai ya amsa zargin da ake masa tun farko, inda kuma kotun ta same shi da laifi.

Shi kuwa Sultan musantawa ya yi abin da ya sa aka yanke shawarar yin zama.

Sai dai a zaman shari’ar na yau, Sultan ya amsa aikata tuhume-tuhumen da ake yi masa.

Kalli Cikakken Video Abun Mamaki da Daurewan Kai da Goge Tunani Kaitsaye 👇 Anan 👇


Post a Comment

Previous Post Next Post