Sai Yau Aka Dawowa ‘yan Shi’a Ababen Hawansu Bayan Shekaru Bakwai da Ragargaje su da Ruguje su Sojojin a Zariya

 Sai Yau Aka Dawowa ‘yan Shi’a Ababen Hawansu Bayan Shekaru Bakwai da Ragargaje su da Ruguje su Sojojin a Zariya

Shekaru bakwai da kisan 'yan'uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky wadanda aka fi sani da ‘yan shi’a fiye da dubu daya a Disambar 2015, daga karshe an bai wa masu ababen hawa daga cikinsu kayansu.

A ranar Asabar 1 ga watan Afrilun 2023 aka bai wa ‘yan shi’ar motocinsu da baburansu da Keke Napep bayan da wata babbar kotu a Kaduna ta bada umurnin hakan bayan kwashe tsawon lokaci ana tafka shari'a.

Sai dai da yawan motocin an farfasa su da harsasai. A yayin da wasu motocin da aka damkawa 'yan sanda ajiyarsu suka sace injinansu, batiransu, tayoyinsu, rima-rimansu da dai sauran su.

Barista M. Abu, lauyan dake wakiltar ‘yan shi’ar a yayin ganawa da manema labarai cikin harshen Ingilishi, ya bayyana cewa; sun zo ofishin ‘yan sanda na MTD ne bisa hukuncin kotu da suka samo a madadin wadanda suka shigar da kara; “wato Harkar Musulunci a Nijeriya wadanda aka fi sani da ‘yan Shi’a. Mun samu hukuncin kotu kan a sakar musu ababen hawansu daga babbar kotun Kaduna. Mun zo nan ne domin tabbatar da an bi wannan hukuncin”, inji shi.


Kalli Cikakken Video Kaitsaye 👇 Anan 👇Da yake karin haske, Barista M. Abu ya ce; “adadin ababen hawan da muka shigar da kara a kai ya zarce adadin wadanda muka gani yanzu a nan. Ababen hawan da ke kasa a nan guda 67 ne kawai. Kuma yakamata a ce sun fi haka. Ko wadanda muka gani a nan duk an lalata su. Bai kamata mu same su a wannan yanayin ba”, ya lurantar.

Lauyan da ya tsayawa ‘yan shi’ar a kotu ya ce bayan abin da ya faru tsakanin ‘yan shi’a da sojoji a Disambar 2015, an kama daruruwan ‘yan shi’a bisa zargin tare hanya tare da ababen hawansu; “wadanda mafi yawa aka kwashe a gefen hanya da kuma gidan Malaminsu, Malam El-Zakzaky. Inda sojoji suka kwace musu ababen hawansu tare da kama mutane wanda suka mikawa rundunar ‘yan sanda domin gudanar da bincike tare da gurfanar da su domin yanke musu hukunci. An tafka shari’a wanda a karshe dukkanin wadanda aka kama aka sake su tare da wanke su daga dukkanin zarge-zarge”.

Ya kara da cewa; “amma a bangaren ababen hawansu wadanda aka ajiye a MTD, kuma ba a taba gabatar da su a gaban kotu ba a lokacin shari’a. Bayan wancan hukuncin mun dauki matakin ganin an bayar da ababen hawan amma suka ki. Dole ta sa muka shigar da kara kan hakan. Sakamakon hukuncin da kotu ta yanke cewa a bayar da ababen hawan ne ya sa muka kasance a nan a yau”, ya tabbatar.


Lauyan ya ce tun cikin shekarar 2022 kotun a karkashin mai shari’a A. A Amina ta bayar da umurin bayar da ababen hawan. “daga lokacin da kotun ta bayar da umurni zuwa yanzu ya dauki lokaci”, inji shi.

Lauyan ya tabbatar da cewa; za su duba matakin da za su dauka a gaba duba da cewa ababen hawan da aka ba su ba su kai wadanda suka shigar da kara suna nema ba.

A yayin zantawarsa da ‘yan jarida, daya daga cikin wadanda suka rasa abin hawansu, Sidi Muhammad Rabiu Kadaure, mazaunin garin Kaduna, ya ce; “kayayyakin kamar yadda muka zo muka same su da yawansu an ciccire abubuwan da suke cikin Babura da motoci, an cire injinansu. Mafi yawan kayayyakin sai dai ka dauki gwangwanin mota ko babur. Kamar ni babur dina ma an cire tayoyin ne ma”, in ji shi.


Injiniya Ahmad Gilima, daya daga cikin wanda ya zo karbar motarsa, ya ce; bayar da ababen hawan ya sake fallasa irin girman zaluncin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta aikata musu.

Wakilinmu ya labarto cewa; mafi yawan masu ababen hawan da aka bai wa kayansu lamarin ya rutsa da su ne a muhallan Husainiyyah Bakiyyatullahi da kuma Gidan Shaikh Zakzaky a Gyallesu.

Wakilinmu da ya halarci wurin bayar da ababen hawan ya tarar da ‘yan Shi’ar da dama ne suka hallara a ofishin 'yan sandan dake lura da tattara ababen hawa na MTD dake karamar Hukumar Sabon Gari a Zariya domin bayar da shaidar abin hawansu domin su dauka. Inda suke cike wani takarda dauke da sa hannun Lauya kafin ba su abin hawansu.


Daga cikin ababen hawan akwai motocin lafiya na agajin gaggawa mallakin 'ISMA Medical Care Initiatives' na Harkar Musuluncin wacce sojojin Nijeriya suka kwashe a Disambar 2015 bayan sun kashe Likitoci da ma'aikatan lafiyan dake kula da wadanda aka jikkata a yayin harin da sojoji suka kai muhallin Husainiyyah Bakiyyatullah, Gidan Shaikh Ibraheem Zakzaky a Gyallesu da kuma Darur Rahma kamar yadda bayanai suka tabbatar.

Ado Sahifa, daya daga cikin wadanda suka bibiyi tabbatar da ganin an bayar da ababen hawan, ya tabbatar mana da cewa; sun karbi motoci 67, babura 10, Keke Napep guda uku.

Rahotanni sun labarto cewa a cikin watan Disambar 2015 ne sojoji suka dira kan mabiya Harkar Musulunci a Nijeriya da aka fi sani da ‘yan shi’a bisa zargin tare wa shugaban Hafsan sojoji na wancan lokaci, Laftanar Janar Tukur Bururai hanya a Zariya. Lamarin da ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi.

Bayanai sun nuna cewa bayan sojoji sun kammala kashe ‘yan shi’ar ne sai kuma suka kwashe dukkanin ababen hawansu suka mikawa rundunar ‘yan sandan Nijeriya.

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da bizne mutum 347 a ramin bai daya, a yayin da bangaren almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky suka ce an kasha musu ‘yan’uwa fiye da dubu daya. Kungiyoyin kare hakkin Bil’adama na Amnesty International da Human Rights Watch sun ce wadanda aka kashe sun fi adadin da gwamnati ta ayyana.

Daga Ammar M. Rajab

Post a Comment

Previous Post Next Post