Video: Dan majalisa Jalingo Taraba da Ya Rasu Ismail Yushau Maihanci (R.I.P)

 Hausa Channel ta rawaito dan majalisar mai wakiltar Jalingo, Yorro, Zing a jihar Taraba, Ismaila Yushau Maihanchi ya rasu.

Rasuwar tasa, kamar yadda twakilinmu ya tattaro, ta faru ne da sanyin safiyar yau Asabar a babban birnin tarayya, FCT.

Kalli Faifan Video Kaitsaye Anan


Da yake tabbatar da rahoton, kakakin jam’iyyar PDP, Andeta’rang Irammae, ya ce jim kadan bayan lashe zaben, zababben dan majalisar ya kamu da rashin lafiya inda yake jinya a wani asibiti a birnin tarayya Abuja.

Da yake bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga jam’iyyarsa, ya ce marigayin ba jam’iyyar kadai bace za ta yi kewar sa , har ma al’ummar jihar baki daya.

Shi ma ana jawabin, mukaddashin shugaban jam’iyyar, Abubakar Bawa, ya bayyana rasuwar a matsayin babban rauni ga ‘ya’yan jamiyyar PDP a jihar da ma kasa baki daya.

Wata majiyar ‘yan uwa da ta zanta da wakilin mu ta tabbatar da cewa marigayin ya kamu da rashin lafiya jim kadan bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben da aka kammala.

Majiyar dangin ta ce za a sanar da shirye-shiryen yin jana’izar nan bada jimawa ba.

Zababben dan majalisar wanda ya fafata a zaben majalisar dokoki ta kasa a karkashin jam’iyyar PDP, ya doke abokan hamayyarsa na jam’iyyar APC, NNPP da SDP da gagarumin rinjaye.

Post a Comment

Previous Post Next Post