Ɗaurarru 75,507 Na Cinye Abincin Naira Biliyan 22.44 Duk Shekara A Gidajen Yari

gwamnatin tarayya na kashe Naira biliyan 22.44 a shekarar ɗaya wajen ciyar da fursunoni 75,507 a gidajen gyaran hali a fadin kasar, in ji wani jami’i a yau Alhamis a Abuja.

Kalli Video Kaitsaye Anan 👇
Babban sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Dr Shuaib Belgore ya bayyana cewa fursunonin sun bazu a cibiyoyin gyaran hali 244 a fadin kasar.

Belgore ya ce kashi 70 na fursunonin ma su jiran shari’a ne

Ya kuma danganta yawan fursunonin da ke jiran shari’a da kamasu ba bisa ka’ida ba, da tsaiko wajen tabbatar da adalci da kuma kasa cika sharuddan beli.

Sakataren ya ce hakan ne ya janyo cunkoso a gidajen yari guda 82 a fadin kasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post